Man United ta daina neman daukar Marko Arnautovic

An wallafa

Manchester United ta daina kokarin dauko dan kwallon Bologna, Marko Arnautovic.

Sabon kocin United, Erik ten Hag na son daukar dan kwallon tawagar Australia, mai shekara 33, wanda ya horar a FC Twente.

An fahimce cewar United ta hakura da cinikin, saboda dogon buri da Bologna ta saka kudin sayar da dan wasan, sannan magoya bayan United sun nuna ba sa bukatar dan kwallon.

An yi ta bayar da rahotannin cewar magoya bayan United ba sa son a dauko musu dan wasan da shekarunsa suka ja na haihuwa.

Ten Hag ya hakura da batun daukar tsohon dan kwallon West Ham da Stoke City, bayan da United ta yi rashin nasara da ci 2-1 a hannun Brighton a wasan farko da fara Premier League ranar Lahadi a Old Trafford.

Christian Eriksen ya fara wasansa na farko a Old Trafford a matakin mai cin kwallo ranar Lahadi, yayin da Marcus Rashford da Jadon Sancho suka buga gefen fili daga gaba a ranar.

Anthony Martial na jinya bai buga fafatawar ba, sai da aka yi hutu United ta saka Cristiano Ronaldo a wasan.

Arnautovic ya ci kwallo 43 a wasa 184 a Premier League tsakanin 2013 zuwa 2019.