Arsenal za ta kara da Bournemouth da Man United da Liverpool a Amurka

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Kociyan Arsenal, Mikel Arteta ya bayyana ƴan wasa 26 da za su buga wa ƙungiyar wasannin atisaye a Amurka, domin shirin tunkarar kakar 2024/25.

Cikin ƴan wasan ta haɗa da ƙwararru da kuma matasan da za su fuskanci Bournemouth da Manchester United da kuma Liverpool.

Ƙyaftin, Martin Odegaard ne zai ja ragamar ƴan wasan da Ben White da Gabriel Jesus da Jurrien Timber da waɗanda suka buga Euro 2024, Leandro Trossard da Jorginho da Jakub Kiwior da kuma Oleksandr Zinchenko.

Sauran sun hada da Emile Smith Rowe da Eddie Nketiah da Fabio Vieira da Reiss Nelson da Karl Hein da sabon ɗan wasa Tommy Setford da Lucas Nygaard da matashi Alexei Rojas.

Ƴan wasan da suka yi nisa a gasar Copa America da Euros 2024 da suka haɗa Gabriel Magalhaes da Gabriel Martinelli da Kai Havertz sai a ranar 27 ga watan Yuli za su je sansanin Gunners a Amurka.

Su kuwa waɗanda suka kai wasan karshe a Euro 2024 da suka hada da Declan Rice da Aaron Ramsdale da Bukayo Saka da David Raya da kuma William Saliba - za su koma Arsenal da zarar ta kammala wasannin da za ta buga a Amurka.

Kieran Tierney da Takehiro Tomiyasu suna jinya, waɗanda za su ci gaba da zama a Landan.

Arsenal za ta fara wasa da Bournemouth a LA Galaxy a Dignity Health Sports Park ranar Laraba 24 ga watan Yuli.

Daga nan za ta fafata da Manchester United a SoFi Stadium a Los Angeles ranar Asabar 27 ga watan Yuli.

Gunners za ta karkare da wasan a Philadelphia da Liverpool a Lincoln Financial Field ranar Laraba 1 ga watan Agusta.

Ƴan wasan da za su buga wa Arsenal wasannin sada zumunta a Amurka

Masu tsaron raga: Karl Hein, Tommy Setford, Lucas Nygaard, Alexei Rojas

Masu tsare baya: Ben White, Oleksandr Zinchenko, Jurrien Timber, Josh Nichols, Jakub Kiwior, Ayden Heaven, Omar Rekik

Masu buga tsakiya: Thomas Partey, Jorginho, Michal Rosiak, Myles Lewis-Skelly, Martin Odegaard, Emile Smith Rowe, Fabio Vieira, Ethan Nwaneri, Salah–Eddine Oulad M’Hand, Jimi Gower

Masu cin ƙwallaye: Leandro Trossard, Reiss Nelson, Charles Sagoe Jr, Gabriel Jesus, Eddie Nketiah