Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Europa League: Liverpool ta lallasa Toulouse, Brighton ta doke Ajax
Liverpool ta ci gaba da taka rawar gani a gasar cin kofin Europa bayan da ta doke kungiyar Toulouse ta Faransa da ci 5-1 a rukunin E.
Masu masaukin baki sun fara jefa kwallo a raga a filin wasa na Anfield ta hannun Diogo Jota a minti na tara da fara wasa.
Toulouse ya mayar da martani ta hannun Thijs Dallinga, amma wataru Endo da Darwin Nunez sun ci wa Liverpool kafin a tafi hutun rabin lokaci.
Ryan Gravenberch ya ci wa Liverpool kwallo na hudu kafin Mohammed Salah wanda ya shigo daga baya ya karasa inda ya ci a cikin karin lokaci.
Nasarar na nufin Liverpool ta tabbatar da matsayinta a saman rukunin E, da maki tara bayan wasanni uku, yayin da Toulouse ta tsaya ta biyu da maki hudu.
Ita kuwa Brighton ta samu nasara ta farko a tarihinta a gasar inda ta doke Ajax da cin 2-0 a yunkurinta na ketarawa zuwa zagaye na gaba.
Yanzu Brighton ta na mataki na uku a rukunin B, maki daya a bayan Marseille da ke jan ragamar rukunin da maki biyar.