Shugaban Afirka ta Kudu ya yi magana kan zargin satar kudi

Ramaphosa

Asalin hoton, Reuters

An wallafa

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ce makomarsa tana hannun jam'iyyarsa, a jawabin da ya yi karon farko tun bayan da aka fitar da rahoto game da badakalar wasu kudade da aka sace daga gonarsa.

'Yan hamayya sun yi kira ya sauka daga mulki bayan wani kwamitin masana shari'a ya bayyana cewa ya karya doka.

Ranar Asabar, mai magana da yawun Mr Ramaphosa ya bayyana cewa shugaban kasar ba zai sauka daga mukaminsa ba.

Yanzu shugaban kasar ya ce manyan jami'an jam'iyyarsa ne za su yanke hukunci kan makomarsa.

Shugabannin jam'iyyar Africa National Congress (ANC) suna ganawa yanzu a Johannesburg domin tattaunawa kan sakamakon binciken da aka gudanar.

Da yake jawabi a wajen dakin taron, shugaban kasar ya ce 'yan kwamitin zartarwar jam'iyyar sun umarce shi da kada ya halarci taron "domin su samu damar yin bayani karara ba tare da katsalandan ba ko kuma fargaba".

Ranar Litinin, babban kwamitin zartarwar jam'iyyar ANC zai gana kan batun.

"Komai ya ta'allaka ne ga Kwamitin Zartarwa na Kasa, wanda nake karkashinsa, ya dauki dukkan matakin da ya ga dama," in ji Mr Ramaphosa a tattaunwarsa da manema labarai.