Chelsea ta sayar da Palmieri ga West Ham United

An wallafa

West Ham United ta kammala sayen mai tsaron baya, Emerson Palmieri daga Chelsea kan kudin da ake cewar ya kai fan miliyan 15.

Mai shekara 28 dan kwallon tawagar Italiya ya koma West Ham kan yarjejeniyar kaka hudu da cewar za a iya tsawaitata idan ya taka rawar gani.

An ce West Ham ta dauki dan kwallon kan kudi da zai fam miliyan 13 da kuma karin fam miliyan biyu na tsarabe-tsarabe.

Dan kwallon ya koma Stamford Bridge da taka leda a 2018 daga Roma, wanda ya je Lyon wasannin aro a kakar da ta ce, bayan da bai samun buga wasanni kamar yadda ya kamata.

Dan kwallon da ya lashe Euro 2020 da Italiya, ya zama na bakwai da West Ham ta saya a bana.

Kungiyar da David Moyes ke jan ragama tana ta karshe a teburin Premier ba tare da maki ba, bayan wasa uku da ta buga a kakar nan.

Cikin 'yan wasan da ta dauka a bana da tsada har da mai cin kwallaye, Gianluca Scamacca daga Sassuolo kan fam miliyan 30 da mai tsaron baya Nayef Aguerd daga Rennes kan fam miliyan 30 da mai cin kwallaye Maxwel Cornet daga Burnley kan fam miliyan 17.5.

Haka kuma ta dauki mai taka leda daga tsakiya Flynn Downes daga Swansea kan fan miliyan 12 da mai tsaron baya Thilo Kehrer da mai tsaron raga Alphonse Areola da kudinsu ya kai fam miliyan 10 daga Paris St-Germain.