Ku San Malamanku tare da limamin Masallacin Jumu'ah na Imam Malik, Jigirya, Kawaji, Kano

Bayanan bidiyo, Taɓa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Ku San Malamanku tare da limamin Masallacin Jumu'ah na Imam Malik, Jigirya, Kawaji, Kano
An wallafa

Ku san Malamanku na wannan karon ya tattauna ne da Sheikh Nuhu Musa Nuhu, limamin Masallacin Jumu'ah na Imam Malik da ke Jigirya unguwar Kawaji a Kano.

A tattaunawarsa da BBC Mallam ya ce yanzu an zo wani zamani wanda ba kowa ne yake tsayawa tsayuwar daka ya wahala ya yi karatun addini kamar yadda magabata suka yi ba.

Ya ce yawanci ana yin ilimi ne na satifiket, ilimin da za a ce Dakta Wane ko Farfesa Wane. Amma ya ce ba ta yadda za a yi jam'i gaba ɗaya.

Asalin Mallam

Mallam ya ce an haife shi a birnin Kumasi ne amma asalinsa dan Najeriya ne. Kasancewar iyayensa sun je Ghana fatauci Allah Ya kaddara aka haife shi a can.

A wannan babban gari na Kumasi ne Mallam ya fara karatun Al'kur'ani tun yana yaro, a wajen wani malami Shehu Muhammad Tijjani.

Bayan ya kai shekara 18 sai Allah Ya yi komawarsa gida Kano, inda a can ne ya shiga makarantar koyar da harshen Larabci da addinin Musulunci, ta SAS da ke cikin birnin Kano.

Tarihin Karatunsa

A tattaunawar tasa da BBC, Mallam ya ce bayan komawarsa Kano daga Kumasi ya ɗan taɓa karatu a wajen marigayi Shehu Mallam Tijjani Zangon-Barebari, inda ya fara karatun Fiqihu har zuwa lokacin da Allah Ya yi wa malamin rasuwa.

Ana cikin haka ne kuma ya fara makaranta ta tsari wato inda ya samu shiga SAS.

Bayan da ya kammala karatunsa a SAS sai aka tura shi garin Ɓagwai inda ya koyar da harshen Larabci da ilimin addinin Musulunci har tsawon shekara biyu.

Yana cikin wannan koyarwa ne kuma sai aka sauya masa makarantar da yake koyarwa inda aka mayar da shi Dawanau a Kanon, inda ya koyar tsawon wata shida.

Malam ya ce a gwagwarmayarsa ta neman ilimi ya yi karatu a Markas da ke Fagge a Kano.

Haka kuma malamin ya je Jami'ar Musulunci da ke Madina a Saudiyya inda ya yi karatu tsawon shekara shida.

Bayan ya kammala Jami'ar Madina ya koma gida Najeriya sai aka tura shi aikin yi wa ƙasa hidima, wato NYSC a maiduguri, amma kuma daga bisani ya koma da aikin Kano inda ya haɗu da marigayi Mallam Aminuddeen Abubakar.

Malaman da ya yi karatu a wurinsu

Malamin ya ce a makarantun da ya yi Allah Ya haɗa shi da malamai da dama, wasunsu fitattu, a Najeriya wasu kuma Larabawa.

Daga cikinsu bayan waɗanda a baya muka bayyana muku, akwai manya da suka hada da, Sheik AbdulKadir wanda mutumin Sudan ne, wanda ya koyar da su Fiqihu.

Akwai Sheik Shahin daga Masar wanda ya ce ya karantar da su ilimin Adab.

Abin da ya fi ba Mallam sha'awa

Mallam Nuhu Musa Nuhu ya ce a yanzu babu wani abu da yake ba shi sha'awa a rayuwarsa wanda ya wuce, ya ga yana yin abin da Allah (SWT) da Ma'aikinsa (SAW) suka umarci a yi.