Abin da ya kamata ku sani kan wasan Arsenal da Everton

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal za ta karbi bakuncin Everton a kwantan wasan Premier League da za su kara ranar Laraba a Emirates.
Wasa ne da ya kamata su fafata tun ranar 11 ga watan Satumbar 2022, wanda ya zama kwantai da za su fafata ranar Laraba.
Sun kara ranar 4 ga watan Fabrairu a Goodison Park, inda Everton ta ci 1-0 ta hannun James Tarkowski a minti na 60 a gasar ta Premier.
Arsenal tana matakin farko da tazarar maki biyu tsakaninta da Manchester City ta biyu, idan ta yi nasara za ta bai wa kungiyar Etihad tazarar maki biyar.
Ita kuwa Everton tana ta 18, wato cikin 'yan ukun karshe a babbar gasar tamaula ta Ingila ta kakar nan.
Arsenal na auna koshin lafiyar Thomas Partey, wanda aka sauya shi a wasan da Gunners ta ci Leicester City a Premier.
Har yanzu Gabriel Jesus da kuma Mohamed Elneny na jinya.
Dan wasan Everton, Dominic Calvert-Lewin bai zai buga fafatawar ba tare da James Garner da Nathan Patterson har da Andros Townsend.
Watakila Arsenal ta zama ta daya a Ingila da ta ta ci kungiya daya wasa 100 a tarihi, kawo yanzu ta doke Everton kawo 99 a fafatawa 99.
Karawa tsakanin kungiyoyin biyu

Asalin hoton, BBC Sport
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Cin da Everton ta yi wa Arsenal 1-0 a Emirates a ranar 23 ga watan Afirilun 2021, shine nasarar da ta yi a wasa 26 da ta kai ziyara da canjaras hudu aka doke ta 21.
Gunners ta doke Everton 5-1 a bara - karo na biyar da ta ci kungiyar kwallo biyar ko sama da haka a Premier League.
Arsenal
Wasa daya Arsenal ta yi nasara daga hudu baya a gida da canjaras biyu da rashin nasara daya, bayan cin 10 a Emirates.
Idan ta yi nasara za ta hada maki 60, karon farko da za ta yi wannan kwazon, bayan wasa 25, wadda ta yi haka a 2003-04 da kakar 2007-08.
Mikel Arteta ya yi rashin nasara a wasa hudu a matakin koci da ya fuskanci Everton - kungiyar da tafi doke shi ita ce Manchester City sau shida.
Everton
Everton ba ta taba cin kungiyar da ta fara wasan mako a matakin ta daya a teburi ba a waje, wadda ta yi canajaras biyar aka doke ta 19.
Nasarar da ta doke wadda take ta daya a kan teburi ita ce 2-1 da ta ci a Wimbledon a Satumbar 1986.
Wasan da Everton ta doke Southampton 2-1, shine kadai ta ci a waje daga 13 da ta fafata a bana mai canjaras biyar da rashin nasara bakawi.
Sean Dyche ya sha kashi a wasan farko tara a matakinsa na koci da ya kara da Arsenal, sai dai daya aka doke shi daga fafatawa shida baya, ya lashe biyu da canajaras uku.
Kungiyar da Dyche ya fuskanci Arsenal da ita ba ta cin kwallo fiye da daya a fafataw 15 da cin kwallo bakwai jimilla.

Asalin hoton, Getty Images










