Real Madrid ta je ta ragargaji Liverpool a Anfield

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Liverpool ta yi rashin nasara a hannun Real Madrid da ci 5-2 a wasan farko zagayen 'yan 16 a Champions League da suka kara a Anfield.

Minti hudu da fara wasa Liverpool ta ci kwallo ta hannun Darwin Nunez, minti 10 tsakani Mohamed Salah ya kara na biyu.

Real ta fara zare kwallo biyu ta hannun Vinicius Junior, sannan Eder Militao ya kara na uku, bayan da aka koma zagaye na biyu.

Karim Benzema ya zura biyu a raga kafin a tashi daga wasan na hamayya.

Wannan shine karo na 10 za su kece raini a tsakaninsu, Real Madrid ta ci shida da canjaras daya, Liverpool ta yi nasara uku.

A bara Real ta ci Liverpool 1-0 a Faransa ta lashe Champions League na 14 jimilla.

Ranar Laraba 15 ga watan Maris Liverpool za ta ziyarci Real Madrid domin buga wasa na biyu a Santiago Bernabeu.

Real Madrid mai Champions League 14 tana ta biyu da tazarar maki takwas tsakaninta da Barcelona a La Liga.

Liverpool mai kofin zakarun Turai shida tana ta tara a teburin Premier League da maki 35.

'Yan wasan Real Madrid da aka je Anfield da su:

Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da Luis López.

Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Odriozola, Lucas V. da Rüdiger.

Masu buga tsakiya: Modrić, Camavinga, Valverde, D. Ceballos, Mario Martín da Arribas.

Masu cin kwallaye: Hazard, Benzema, Asensio, Vini Jr., Rodrygo da Álvaro.

Wasa 10 da aka yi tsakanin Liverpool da Real Madrid:

Jurgen Klopp Carlos Ancelotti

Asalin hoton, Getty Images

2022/23 Champions League

  • Liverpool 2 - 5 Real Madrid

2021/2022 Champions League

  • Liverpool 0 - 1 Real Madrid

2020/2021 Champions League

  • Liverpool 0 - 0 Real Madrid

Champions League

  • Real Madrid 3 - 1 Liverpool

2017/2018 Champions League

  • Real Madrid 3 - 1 Liverpool

2014/2015 Champions League

  • Real Madrid 1 - 0 Liverpool

Champions League

  • Liverpool 0 - 3 Real Madrid

2008/2009 Champions League

  • Liverpool 4 - 0 Real Madrid

Champions League

  • Real Madrid 0 - 1 Liverpool

1980/1981 European Cup

  • Liverpool 1 - 0 Real Madrid