Man United za ta fafata da Sevilla a Europa League

Europa League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Manchester United da Sevilla za su kara a wasan quarter final a gasar zakarun Turai ta Europa League.

United ta kawo wannan matakin bayan da ta yi nasara a kan Real Betis da cin 5-1 gida da waje.

Ita kuwa Sevilla ta kai bante ne da cin Fenerbahce ta Turkiya 2-1 a wasa gida da waje.

Jadawalin quarter finals a Europa League

  • Manchester United da Sevilla
  • Juventus da Sporting
  • Feyenoord Rotterdam da Roma
  • Bayer Leverkusen da Royale Union Saint Gilloise

Wasannin farko a quarter finas:

Ranar 13 ga watan Afirilun 2023

  • Manchester United da Sevilla
  • Juventus da Sporting
  • Feyenoord Rotterdam da Roma
  • Bayer Leverkusen da Royale Union Saint Gilloise

Sevilla ce za ta fara zuwa Old Trafford domin buga wasan farko ranar 13 ga watan Afirilu, sannan United ta je Sifaniya wasa na biyu ranar 20 ga watan Afirilu.

Kungiya ta uku da United daga Sifaniya da United za ta fafata da ita a Europa League a kakar nan.

United ta hadu da Real Sociedad a cikin rukuni na biyar da suka hadu gida da waje, inda kowacce ta kare da maki 15 a rukunin, amma Sociedad ce ta daya.

Hakn ne ya sa United ta buga wasan neman gurbin ci gaba da zagayen 'yan 16 da Barcelona, inda United ta kai zagayen gaba.

Daga nan ne United ta ci Real Betis 5-1 gida da waje a karawar 'yan 16 da suka raga a Europa, yanzu za ta fuskanci Sevilla ida da waje.

Sevilla ita ce kan gaba a lashe Europa Leagu mai shida, ita kuwa United daya ne da ita, wanda ta lashe a 2016/17 karkashin Jose Mourinho.

Za a fara wasan farko a quarter-final ranar 13 ga watan Afirilu, sannan karawa ta biyu ranar 20 ga watan Afirilu.

Za a buga wasan daf da karshe ranar 11 ga watan Mayu, sannan wasa na biyu ranar 18 ga watan Mayu.

Za a buga wasan karshe a Budapest a Puskás Aréna ranar 31 ga watan Mayu.

Eintracht Frankfurt ce mai rike da kofin, wadda ta ci Celtic 5-4 a bugun fenariti, bayan da suka tashi 1-1.