Remo Stars ta je ta ci Kano Pillars a jihar Katsina

Asalin hoton, Kano Pillars FC
Kano Pillars ta yi rashn nasara da ci 2-0 a hannun Remo Stars a wasan mako na uku a Premier ta Najeriya da suka kara ranar Lahadi a jihar Katsina.
Pillars tana yin wasanninta na gida a jihar Katsina, sakamakon gyara da ake yiwa filinta na Sani Abacha da ke kofar mata a jihar Kano, Najeriya.
Remo ta fara cin ƙwallo ta hannun Sadik Ismail a minti na 26 da fara wasan, daga baya Franck Mawuena ya kara na biyu.
Karon farko da Pillars ta yi rashin nasara a bana karkashin sabon koci, Usman Abdallah, wanda aka bai wa aikin kan fara kakar nan.
Pillars ta fara da cin Ikorodu United 3-0 a makon farko a jihar Katsina, sannan ta je ta samu maki a Bayelsa United.
Pillars, wadda ake kira sai masu gida za ta buga wasan gaba da Abia Warriors a karawar mako na huɗu a babbar gasar tamaula ta Najeriya.







