Mace Musulma da ta raini mabiya addinin Hindu

An wallafa

Fim din wata Musulma da aka shirya a Jihar Kerala a kudancin Indiya wadda ta raini wasu yara mabiya addinin Hindu uku ya ja hankalin al'umma, saboda labarin iyalai ne da ba a fiye jin irinsa ba.

Wakilin BBC na Hindi, Imran Qureshi ya tattauna da wasu 'yan uwa biyu da fim ɗin ya yi wa ƙaimi.

Ya yin da Jafferkhan ya fara kallon fim ɗin mai suna Ennu Swantham Sreedharan bai san lokacin da ya fashe da kuka ba.

A gefensa lokacin da yake kallon fim ɗin akwai ɗan uwansa da ake kira da Sreedharan, wanda shi ma ya yi ta kuka kamar zai mutu.

Jafferkhan da Sreedharan, dukkansu suna amfani da suna ɗaya ne, kuma shekarunsu 49, ba 'yan uwa ba ne na jini, Jafferkhan Musulmi ne shi kuma Sreedharan mabiyin addinin Hindu ne.

Lokacin da na tambayi Jafferkhan matsayin Sreedharan a wurinsa sai ya ce: "Dan uwa ne a wurina. Ya ma wuce haka. Ko da yaushe yana gefe na. Ban san yadda zan bayyana maka shi ba sama da haka..

Matar da ta kawo su tare - ita ce mahaifiyar Jafferkhan, Thennadan Subaida wadda ta mutu a 2019. Labarinta wanda ya taɓa zukata, ya matuƙar tunatar da mutane kan mutuntaka sama da banbancin addini, ya samu tagomashi yayin da rabuwar kai da tashe-tashe ke faruwa a India akai-akai.

Subaida ta ɗauki Sreedharan da yayyansa mata guda biyu - Ramani da Leela a 1976 bayan mahaifiyarsu ta je haihuwar yaro na huɗu wanda suka mutu tare.

'Yan uwan sun ce Subaida ba ta ɗauki yaran ne ba bisa ƙa'ida ba, dukkuwa da cewa dokokin ɗaukar yaran ba su yi tsauri ba a wancan lokacin.

Sun ƙara da cewa babu wani daga cikin 'yan uwansu da ya nuna sha'awar kula da su, shi ya sa mahaifunsu ya amince Subaida ta ɗauke su, a cewarsa "ba zai iya ɗaukar nauyinmu ba".

Subaida ita kanta na da 'ya'ya biyu, Jafferkhan da yayansa Shanawas a lokacin, kuma daga baya ta haifi 'yarta Joshina, bayan shekara huɗu. Yaran duka sun tashi tare cikin matuƙar haɗin kai.

Bayan mutuwar Subaida a 2019, labarinsu sai ya karaɗe faɗin India - Sreedharan wanda yake aiki a Oman a lokacin ya yi rubutu mai jan hankali a shafinsa na Facebook, inda ya nemi abokansa su yi wa Ummansa addu'a.

Bayanin nasa ya ja hankalin mutane da dama, inda suka riƙa mamakin yadda mutumin da yake da sunan mabiya addinun Hindu amma yana kiran mahaifiyarsa Umma.

"Sun riƙa tambaya wanene kai, mabiyin addinin Hindu ko Musulmi? Abin a buɗe yake sunana Sreedharan," in ji shi.

Tambayoyin ba su da adadi wani lokacin na izgili ne, Amma Sreedharan ya riƙa amsa tambayoyin cikin haƙuri duk da cewa yana cikin jimami.

Ya kuma bayyana yadda Subaida da mijinta Abdul Aziz Haji ba su taɓa neman tursasa mi shi ya musulunta ba.

"Abin takaici ne a wurina rashinta. Iyayena ko da yaushe suna nuna mini banbance-banbance da kuma addini ba wani abun ɗaga jijiyoyi ba ne a wuri ba," in ji shi.

"Kyakkyawar zuciya muke buƙata. Mu mutane ne muke sauya yadda tsarin imani da abubuwa suke."

Wannan shi ne abin da Subaida ta rayu a kai, kuma ita ce aƙidar da ta ɗora yaranta a kai.

Leela da take shekara 51 yanzu, tace mahaifiyar tasu tana ɗaukarta zuwa wajen bauta, "lokacin babu ci gaban ababan hawa sosai, tana ɗauka ta zuwa duk inda take so a lokutan bukukuwan addini - kuma cikin tawaga duk suke zuwa.

"Ummta ko da yaushe na cewa ba wata matsala ba ce, ace mutum yana bin addinin Hindu ko Musulunci ko Kiristanci. Ko wanne addini yana koya mana abu guda, wanda shi ne soyayya da mutunta juna," in ji Sreedharan.

Dan uwansa na da labarai da dama game da yarintarsu da yadda suka tashi.

Shanawas ya ce yana tuno ranar farko da mahaifiyarsa ta dawo gida ɗauke da yaro ɗan shekara biyu, Sreedharan.

"Leela da Ramani na bayanta. Mahaifiyarmu ta ce za su zauna tare da mu tun da ba su da wanda zai lura da lamarinsu," in ji shi.

Bayan wannan dukkansu sun zama 'yan uwan juna.

Shanawas na tuno lokacin da suke barci tare da juna a dandagaryar siminti; da kuma irin murnar da suka yi lokacin da aka haifi Joshina.

Lokacin da suke tashi tare, shaƙuwar da ke tsakanin Sreedharan da Jafferkhan ta sa sun zama "tamkar 'yan biyu" waɗanda suke yin komai na su tare.

Shanawas da Jafferkhan sun ce abu ne mawuyaci kaji su suna faɗa, "duk da cewa kowa ya san mahaifiyarsu ta fi son Sreedharan" a mafi yawan lokuta takan ba shi kulawa ta musamman.

"Ba kamar ni ba, Sreedharan shi ne mai kaiwa da karɓo saƙo a kullum amma mutum ne mai matuƙar gaskiya da amana.

Wataƙila shi ya sa Umma take son shi da yawa," in ji Jafferkhan yana faɗi yana dariya.

Yan uwan junan sun ce sun koyi darasi mai yawa daga rayuwar da suka yi da mahaifiyarsu. Misali Shanawas ya ce yana iya tuna yadda mahaifiyarsu take kyalesu domin ta taimakawa wasu, duk da banbancin da suke da shi na ƙabila da addini.

"Kowa na iya zuwa wajen mahaifiyata ya tambaye ta kuɗi domin neman ilimi da aure da kuma lura da lafiya, da yawan lokuta tana iya ƙoƙarinta domin samar da kuɗin - wani lokacin bashi take karɓa ta basu daga baya sai ta biya," in ji shi.

Wannan ne jigon labarin fim ɗin Ennu Swantham Sreedharan wanda Siddik Paravoor ya shirya.

Paravoor na ɗaya daga cikin mutane da bayanan da Sreedharan ya wallafa a facebook kan mahaifiyarsu ya ƙara wa ƙaimi.

"Akwai darusa da dama na koyarwar rayuwa a cikin fim ɗin da al'umma ya kamata su koya" ya ce ya taɓa bangaren alaƙar mutane duk da sauye-sauyensu.

An yi wa fim ɗin kallo na musamman a sinima a Kerala a ranar 9 ga watan Janairu. Oaravoor yanzu na ƙoƙarin tara kudi ne da zai saki shi a kasuwa.

'Yan uwan waɗanda yanzu suke rayuwa a wurare daban-daban sun ce ba za su iya yin ta'aziyya ga mahaifiyarsu ba yadda ya kamata.

"Ina tuna wasu lokuta masu daɗi tare da Ummana. In na tuna babu ita yanzu abin na sosan rai, amma daɗin da nake ji da wannan fim za a riƙa tuna mahaifiyata," in ji Leela.

"Sai da mahaifiyarmu ta rasu mutane suka gano banbancin da ke tsakaninmu," a cewar Shanawas.

"Amma har gobe bamu da banbanci da juna."