Sojoji sun sake yin juyin mulki a Burkina Faso

An wallafa

Sojoji a Burkina Faso sun hamɓarar da shugaban gwamnatin sojan ƙasar, Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba ranar Juma'a, bayan ya hau mulki a watan Janairun da ya gabata.

Kaftin Ibrahim Traore ya sanar ta kafar talabijin ɗin ƙasar cewa sun tumɓuke shugaban ne saboda ya gaza magance hare-haren masu iƙirarin jihadi a ƙasar da ke Afirka ta Yamma.

Sanarwar ta ce an rufe dukkan iyakokin ƙasar na ƙasa daga Juma'a da dare.

Haka nan sun dakatar da aiki da kundin tsarin mulkin ƙasar da kuma rusa gwamnati mai-ci.

A watan Janairu ne Kanar Damiba ya hau mulki bayan ya jagoranci juyin mulki, inda ya hamɓarar da zaɓaɓɓiyar gwamnati bisa zargin ta kasa daƙile hare-haren 'yan bindigar masu iƙirarin jihadi.

Tun da farar safiyar Juma'a aka ji ƙarar harbe-harbe a kusa da Fadar Shugaban Ƙasar Burkina Faso da kuma hedikwatar sojojin juyin mulki, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato shaidu suna cewa.

Sojoji sun tare manyan hanyoyin da suke babban birnin ƙasar Ouagadougou.

An jibge dakarun tsaro a manyan hanyoyin da ke yankin da fadar shugaban ƙasar da hedikwatar sojojin suke.

'Yan bindigar da ke da alaƙa da ƙungiyoyin al-Qaeda da kuma ISIS sun fara kai hare-hare ne a 2015, abin da ya yi sanadiyyar kashe dubban mutane da kuma raba kusan miliyan biyu da muhallansu.