An ji ƙarar harbe-harbe a Fadar Shugaban Ƙasa a Burkina Faso

An wallafa

An ji ƙarar harbe-harbe a ranar Juma'a da sassafe a kusa da Fadar Shugaban Ƙasar Burkina Faso da kuma hedikwatar sojojin juyin mulki, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato shaidu suna cewa.

Sojoji sun tare manyan hanyoyin da suke babban birnin ƙasar Ouagadougou.

An jibge dakarun tsaro a manyan hanyoyin da ke yankin da fadar shugaban ƙasar da hedikwatar sojojin suke, in ji AFP.

Fargaba a Burkina Faso bayan wani mummunan hari

Yanayin da ake ciki a Burkina Faso na da rikitarwa kuma ba a san waye ya bayar da umarnin jibge sojoji a kusa da fadar shugaban kasar a babban birnin na Ouagadougou ba.

An kuma ji ƙarar harbe-harbe a barikokin soji ba.

Sai dai an ce an ga gawar sojoji 11 da fararen hula 50 a ranar Litinin a garin Djibo da ke arewacin ƙasar bayan wani kwanton ɓauna da aka yi musu.

A watan Janairu ne Laftanal Kanal Paul-Henri Sandaogo Damiba, ya ƙwace mulki, inda ya yi alkwarin murƙushe masu tsattsauran ra'ayi da ke tayar da ƙayar baya tun shekarar 2015, amma har yanzu rikici na ci gaba da ƙamari.

Harbe-harbe a barikokin soji - rahotanni

Wata kafar yaɗa labaran ƙasar ta ce an ji ƙarar harbe-harbe a barikokin soji a garuruwa daban-daban a fadin Burkina Faso.

Kafar yaɗa labaran ta Actualite Burkina Faso, ba ta faɗi sunayen garuruwan ba.

Rahotannin farko-farko sun ce kawai dai an ji ƙarar harbe-harbe a manyan barikokin sojin da ke birnin Ouagadougou.

Gidan talabijin na gwamnatin ƙasar bai buɗe ba kuma an tsaurara matakan tsaro na shiga gidan rediyon gwamnatin ƙasar.

Shugaban Burkina Faso na lafiya - rahotanni

Yanayin da ake ciki a Ouagadougou na da ruɗarwa bayan jin ƙarar harbe-harbe.

Sojoji masu ɗauke da makamai sun barbazu a muhimman wurare a babban birnin.

Shugaba mulkin soji na ƙasar Kanal Paul-Henri Damiba, wanda ya ƙwace iko da mulkin a watan Janairu, "yana babban birnin cikin halin lafiya," a cewar rahotannin kafar yaɗa labarai ta Jeune Afrique reports.

Ƴan sanda ba su san me ke faruwa ba - rahotanni

Wani ɗan jarida a Ouagadougou ya ruwaito cewa sojoji sun toshe wata babbar hanya a kusa da ofishin firaminista kuma suna hana mutane shiga gine-ginen gwamnati.

Mafi yawan sojojin sun sanya takunkumin fuska, in ji ɗan jaridan, ya ƙara da cewa jami'an ƴan sanda sun ce ba su san me yake faruwa ba.

"Mutane da dama suna ci gaba da harkokinsu," ya ce.