Odegaard ba zai buga wa Norway Nations League ba

Asalin hoton, Getty Images
Ƙyaftin ɗin Arsenal, Martin Odegaard ya ce ya kamata ya kara murmurewa, kenan ba zai yi wa Norway wasan Nations League ba.
Mai taka leda daga tsakiya ya ji rauni a cikin watan Satumba lokacin da yake buga wa tawagar sa tamaula, hakan ya sa ya yi jinyar mako bakwai.
Ya koma taka leda a wasan da Arsenal ta yi rashin nasara 1-0 a Inter Milan a Champions League a makon jiya, wanda ya shiga karawar daga baya.
Sai dai Gunners ta fara wasa da Odegaard ranar Lahadi a Premier League da Arsenal ta tashi 1-1 da Chelsea a Stamford Bridge.
Norway za ta fafata da Slovenia a Nations League ranar Alhamis 14 ga watan Nuwamba, kwana uku tsakani ta kece raini da Kazakhstan.
To sai dai Odegaard ya ziyarci birnin Oslo, domin a ci gaba da auna koshin lafiyarsa.
Ranar Asabar 23 ga watan Nuwamba Arsenal za ta karɓi bakuncin Nottingham Forest a gasar Premier League a Emirates.
Daga nan kuma Gunners za ta je gidan Sporting a gasar Champions League ranar Talata 26 ga watan Nuwamba.










