Tsananin sanyi na kashe jarirai a Gaza

Hukumar lafiya da Hamas ke gudanarwa a Gaza ta ce jarirai sababbin haihuwa na Falasdinawa shida ne suka rasu sakamakon kamuwa da tsananin sanyi a cikin mako biyu.
Mahaifiyar daya daga cikin jariran wadda ta sheda wa BBC yadda jaririyar ta kamu da larurar ta ce sama da sau goma sojojin Isra'ila na tilasta musu sauya matsuguni cikin wata 14 na yakin, a yanayi na tsananin huturu da rashin muhalli mai kyau da kuma rashin abubuwan rayuwa.
Bayanai sun nuna yadda aka samu mace-macen a asibitoci bayan jariran sun kamu da cutar a sansanonin gudun hijra da suke zaune a dalilin yadda sojin Isra'ila ke tilasta musu sauya matsuguni a tsawon wannan yaki, kamar yadda iyalan suka bayyana.
Mahaifiyar daya daga cikin jariran, Sila, wadda take kasa da mako uku da haihuwa, ta sheda wa BBC yadda ta gano halin da jaririyar tata ta kamu da cutar ta tsananin sanyi.
Nariman al-Najmeh, wadda ta ce, da wata Safiya ne kawai ta lura cewa jaririyar ta kame ba ta ko kifta ido, kuma fuskarta ta yi launin shudi, ta sheda wa BBC yanayin tantin da suke zaune;
''Ban taba tunanin zan haihu a tanti a cikin irin wannan yanayi na tsananin sanyi ba, kuma ruwa na yoyo a kanmu. Tantin na yoyon ruwa. Wani lokacin ma sai dai mu gudu domin kada ruwan ya shafi lafiyar jaririyar,'' in ji mahaifiyar.
Matar da mijinta da ke sana'ar kamun kifi da kuma sauran 'ya'yansu biyu, suna zaune ne a sansanin 'yan gudun hijira da ke bakin teku a kudancin Gaza.
Nariman ta kara da cewa suna rayuwa ne cikin yanayi na rashin kusan komai ko da lokacin da ta samu juna biyu tana ma tunanin yadda za ta samu tufafin da za ta sanya wa abin da za ta haifa saboda mijinta ba shi da wani aiki yanzu da yake yi.
Isra'ila ta hana kafafen yada labarai na duniya shiga da kuma aiki a yankin na Gaza cikin walwala.











