Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Busquets ya zama kan gaba a yawan buga El Clasico a tarihi
Real Madrid ta yi rashin nasara a hannun Barcelona da ci 1-0 a Santiago Bernabeu a wasan farko a daf da karshe a Copa del Rey.
Kyaftin din Barcelona, Sergio Busquets ya buga wasan na hamayya kuma karo na 46 a tarihi.
Hakan ya sa ya haura Lionel Messi da Sergio Ramos, wadanda suka buga El Clasico 45 kowanne.
Yanzu Messi kyaftin din tawagar Argentina na taka leda a Paris St Germain, Ramos tsohon dan kwallon Real shima yana PSG.
Busquets ya fara yin wasan El Clasico a cikin Disambar 2008, karkashin Pep Gueardiola, inda Barcelona ta ci Real Madrid 2-0 a fafatawar.
Sau 43 Barcelona ta fara wasa da Busquets a cikin fili a karawa da Real Madrid, sannan ya yi canji karo uku.
Sai dai kyaftin din bai taba cin kwallo ba a wasannin El Clasico, amma an yi nasara da shi 22 da canjaras takwas aka doke Barca sau 16 yana cikin.
A cikin kakar nan Busquets zai kara fuskantar Real Madrid a wasan El Clasico ranar 19 ga watan Maris a fafatawar La Liga a Camp Nou.
Real Madrid za ta kai ziyara Barcelona a was ana biyu a Copa del Rey wasan daf da karshe ranar 5 ga watan Afirilu.
Real ce ta fara cin Barca 3-1 cikin watan Oktoba a La Liga a Bernabue, Barca ta ci Real 3-1 cikin Janairu ta lashe Spanish Super Cup a Saudi Arabia.