Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tsohon golan Ingila Joe Hart zai yi ritaya daga kwallo
Golan Celtic Joe Hart zai yi ritaya a ƙarshen wannan kakar, ya ce yana jin cewa ba dai shi da wata matsala a jikinsa amma yana so ya ajiye takalminsa.
Tsohon golan na Ingila da Manchester City mai shekara 36, ya shaida wa Celtic cewa wannan kakar ta uku da yake yi a ƙungiyar za ta zama kakarsa ta ƙarshe.
Kocin ƙungiyar Brendan Rodgers ya ce Hart da ya buga wa Ingila wasa 75, za a yi kewarsa a wannin gaba.
A matsayin wanda ya yi nasara ta fuskoki biyu, Hart ya lashe kyautuka a City da kuma Celtic.
Ya shaida wa gidan talabijin na Celtic cewa: "Ina son isar da sako cewa zan daina buga kwallo daga yanzu. Wannan wani abu ne da na dade ina tunani a kai, ba wani maganar lokaci ya yi ko bai yi ba cikin lamari".
Hart ya buga wasa 690 tun daga inda ya fara wasa a Shrewsbury, Tranmere, Blackpool, Birmingham, Torino, Burnley da kuma Tottenham.