Marmoush ya ci Newcastle ƙwallo uku rigis a Premier

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Omar Marmoush ne ya ci wa Manchester ƙwallo uku rigis daga 4-0 da ta doke Newcastle United a Etihad ranar Asabar a Premier League zagaye na 25.

Marmoush, wanda ya koma City kan £59m daga Eintracht Frankfurt ya ci ƙwallayen tun kan hutu, wanda ya zura ta farko a minti na 19 da a minti na 24 da a minti na 33.

Kenan wannan shi ne karo na huɗu da aka ci ƙwallo uku rigis a Premier League a kankanin lokaci daga wajen ɗan wasan Manchester City.

Sergio Aguero ya ci uku rigis a babbar gasar tamaula ta Ingila a cikin minti tara a 2015.

James McAtee shi ne ya ci wa City ƙwallo na huɗu, saura minti shida a tashi daga karawar da ya bai wa ƙungiyar Etihad maki ukun da take bukata.

City ta buga karawar ba tare da fitattun masu tsare mata baya ba da ya haɗa da Manuel Akanji da Ruben Dias da kuma Nathan Ake.

Haka kuma Erling Haaland wanda shi ne ƙyaftin ɗin City a wasan, ya ɗan bugu da ta kai an sauya shi, Pep Guardiola zai yi fatan bai ji rauni mai muni ba.

City za ta je Real Madrid ranar Laraba 19 ga watan Fabrairu, domin buga wasa na biyu na cike gurbi a Champions League.

A makon jiya Real Madrid ta yi nasara 3-2 a kan City a Etihad a wasan farko a cike gurbi a gasar ta zakarun Turai.

Newcastle ta yi rashin nasara 16 a jere a Etihad, har da kasa zura ƙwallo a raga a wasa shida baya da ta kai ziyara.