Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Babu abinci a lokacin da na haihu': rashin abinci mai gina jiki na ƙaruwa a Gaza saboda hare-haren Isra'ila
- Marubuci, Fergal Keane
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Jerusalem
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
A yaƙi a wasu lokutan ana ganin abubuwa da dama da suke matuƙar tayar da hankali.
A asibitin Nasser wani jariri ne ɗan wata biyar da ya kasa yin kuka.
Muryar Siwar Ashour ta dashe, tana magana da murya cikin sanyi saboda rashin kuzari da za ta iya yin magana. Ba za ta iya karɓar madara ba, kuma likitoci sun ce hana shigar kayan agaji, da Isara'ila ta yi tsawon wata uku ya haifar da wahalar samun irin nau'in abincin da ta ke buƙata.
Siwar dai na rayuwa ne tamkar yaƙin da neman ƙarar da rayuwarta.
Mahaifiyarta Najwa mai shekara 23, na canjawa Siwar ƙunzugun yara. Nauyinta 2KG (4lb 6oz).
"Babu abinci, a lokacin da na haife ta,' in ji Najwa.
"Ba ni da sinadaran gina jikin da ake buƙata da za su inganta mata lafiya... Yanzu kawai iya madarar yara ta ke sha, kuma ba mu san ta yadda za mu iya samar mata da ita ba."
Isra'ila ta hana ƴan jaridar duniya shiga Gaza don bayar da rahoton abubuwan da ke faruwa.
Wani abokin aikina da ke zaune a can ne ra kalato abubuwan da ke faruwa da ke nuni da ƙaruwar ƙarancin abinci mai gina jiki a jikin Siwar. Kanta ya fi ƙarfin jikinta saboda girma, sannan sandan hannu da na kafa sun koma tamakar silin kara. Tamkar fatar ce ta lulube ƙasusuwan haƙarƙarinta, idan tana ƙoƙarin yin kuka.
Najwa ta damu kan abun da ka iya faruwa, lokacin da tilas ta bar asibitin.
"Asibitin na shan matuƙar wahala wajen samar da madarar yara, sun bincika asibotoci masu yawa, amma a wani guda ɗaya suka samo. Sun sanar da ni cewar za su ba ni kwalba ɗaya idan za mu tafi, amma da ƙyar ta kai kwana huɗu. Mahaifinta makaho ne, ba zai iya siyo mata madarar ba, kuma ko da ma za a iya samun madarar, za a same ta ne da matuƙar tsada, kuma ba shi da aikin yi."
A cewar likitan Siwar Zaid al-Majaida, wannan shi ne karo na biyu da aka kwantar da ita a asibiti. An kuma sake dawo da ita asibitin ne saboda ƙarancin madarar yara.
"Babu wani abu da ke shigowa ta kan iyaka, babu madara, babu abinci. Hakan ya haifar da gagarumar matsala ga yara da ke nan. Wannan jaririyar na buƙatar madara ta musaman wadda za ta gina musu jiki. Akwai ta a baya, amma saboda rufe iyaka da aka yi, yanzu ana ƙanfar kayan, bayan da suka ƙare."
Asibitin na ƙoƙari wajen samo ƙarin abinci, amma Siwar ta yi rauni sannan tana fama da gudawa akai kai.
"idan ta ci gaba da kasancewa a wannan hali, rayuwarta na ciki haɗari, ammam idan ta sami madara mai gina jiki, ko kulawa daga asibiti, zaa iya samun ci gaba a ɓanagaren lafiyar jikinta," in ji Dr Majaida.
Tun a farkon shekara, a cewar majalsar ɗinkin duniya akwai rahoton ƙarancin abinci mai gina jiki a tsakain fiye da yara dubu goma, da aka iya ganowa. Farashin kayan abinci ya yi tashin gauron zabi da kashi 1,400 cikin ɗari.
Wajen bayar da abinci na jinƙai, da ke taimakawa dubban al'ummar Gaza, suma yanzu suna fuskantar yankewar kayan abinci. Wajen gashin burodi da makamantansu, da ke samun tallafi daga hukumar samar da abinci ta duniya suma yanzu sun rufe.
A kudancin binrin Khan Younis, idan asibitin Nasser yake, wakilinmu ya ziyarci wani wajen girka abinci da ƙungiya wasu matasa Shabab Gaza, da ke kai abinci kai tsaye ga iyalai daban-daban. Yadda zai wadatar da kowane iyali a kowacce rana.
Shugaban ƙungiyrar agajin Mohammad Abu Rjileh, ya ce uku daga cikin ɗakin girka abincin nasu yanzu sun rufe su, saboda rashin kayan abinci.
"Kungiyo masu yawa da ke taimaka mana, an sace musu kayan da ke wajen da suke ajiye kayan abinci. Maimakon mu samu sinadaren da za mu dafa anincin mutum dubu 10 a rana, sannan kuma su kai ƙarin wasu mako 10, yanzu iya na kwana biyu muke da su, haka ne zai tilasta mana dakatar da dafa abincin."
Isra'ila ta ta yanke kai dukkan kayan jinƙai da sauran kayan masu mahimmanci zuwa cikin Gaza, tun a ranar 2 ga watan Maris, sannnan ta koma kai hare-hare da amfani da soji mako biyu da suka gabata, suna masu cewar suna matsa lamba ne ga Hamas su sako Isra'ilawa da suke riƙe da su a Gaza, daga cikin har da 24 da har yanzu suke hasashen suna nan da rai.
Majalisar Ɗikin Duniya ta ce matakin Isra'ila na hana kayan agaji shiga Gaza "cin zali ne," akan fararen hula.
Darkatan kula da harkokin jinƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya, kuma tsohon jakadan Birtaniya Tom Fletcher, ya ce dokar ƙasa da ƙasa abu ne da babu kokwanto a cikinsa.
Na yi wa Boaz Bismuth tamabaya kan wannan batu, wanda ɗaya ne daga cikin manyan jami'ai a jam'iyyar Likud ta Firaminista Benjemin Netanyahu. Ya musanta cewar akwai matsala wajen shigar kayan jinƙai, sakmakaon hana kayan da jinƙai, shiga Gaza.
"Akwai abinci a Gaza.. Isra'ila ba za ta taɓa hana shigar da kayan jinƙai ba, idan mutane na buƙatar abinci."
Na kuma sake tambayarsa kan hujojin da muke da su na mutanen da suke mutuwa sakamakon ƙarancin abinci, ciki har da yara da ke cikin yunwa.
"Akwai yara da ke cikin tsananin yunwa. Ya ce akwai irin wannan zargi wata guda da ya gabata na fama da yunwa, da kisan ƙare dangi, sai ya ce "ƙanzon kurege ne".
"Abin da muke so shi ne a sako mutanenmu da Hams ke riƙe da su a Gaza. Idan suka yi haka za a dakatar da yakin cikin daƙiƙa 30."
Tsawon lokaci Isra'ila ta zargi Hamas da karɓe iko da kayan agajin, wani zargi da Hamas ta musanta.
Shugaban mutanen yankin Falasɗinu Mahmoud Abbas da ke yankin zaune da gaɓar yamma da kogin Jordan, ya yi da'awar cewar mafi akasarin kayan agajin da ake sacewa, wasu ƙungiyoyi da ke da alaƙa a Hamas ne ke yi san amma ba Hamas ba.
Ya kira ƙungiyoyin da "yaran karnuka" sannan ya buƙaci da su saki Isra'ilawan da suka riƙe a matsayin fursunoni. Hamas ta mayar da martani, inda suka yi musun cewa Abbas "ya sha ɗora alhakin kan laifukan da Isra'ila ke aikatawa kan mutanensu".
Saboda rashin damar shiga Gaza, tare bayar da rahoton ainihin abun da ke faruwa, zai yi wuya bincike ya bayar da ainihin abun da ke faruwa a zirin na Gaza.
An sha bayyana ƙungiyoyin gagan masu aikata manyan laifuka da hannu ƙarar daga satar kayan agajin. Hamas ta yi barazana kan dukkan ƙungiya ko ɗaiɗaiku da ake zarginsu da satar kayan agajin.
Mutum biyu ne dai aka halaka a bakin wani babban wajen ajiye kaya na UNRWA, amma sai dai abin da bai futo fili ba, shi ne wanda ya kashe su ɗin. Wani ɗan gwagwarmaya ya da ke wajen sanda lamarin ya faru, ya ɗora laifin akan Hamas.
"Hamas na ɓoye abinci, wanda hakan na hana al'umma samun abinci, da siyar da shi da tsada. Al'umma dai sun koka sannan sun buƙaci da a raba abinci ko kuma sun karɓe shi ta ƙarfin tsiya. Hams dai ta harba harsashi kan mutanend a fama da yunwar, a cewar Moumen al-Natour, ani lauyan kuma wanda ya jagoranci zanga-zangar.
Hakan dai na faruwa ne yayin da ake ci gaba da samun ƙaruwar yauna, da rashin doka da oda, sakamakon yaƙin da ake yi a Gaza da hana shigar kayan agaji yankin.
Majalisar Zartarwa ta Isra'ila ta amince da kai hare haren soji a Gaza. Ta ce burinta shi ne lalata Hamas, wani buri da zasu iya cimma masa tun a watannin 19 da suka shafe suna yaƙin.
Akwai kuma rahotanni da ke cewar Isra'ila na shirin amfani da jami'an tsaro na kamfanoni masu zaman kansu don sanya idanu kan rabon kayan agaaji a Gaza, sai dai har yanzu ba sanar da ranar da za a fara waitar da hakan ba.