Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An zargi Isra'ila da kai wa jirgin ruwa da ke son zuwa Gaza hari
Ƴan gwagwarmayar da ke shirin tuƙa jirgin ruwa zuwa Gaza sun ce wani jirgi maras matuƙi ya kai wa jirgin nasu hari a tekun Malta - inda suke zargin Isra'ila da cewa ita ce ta kitsa harin.
Ƙungiyar ƴan gwagwarmayar mai suna Freedom Flotilla Coalition ta ce an hari jirgin nata mai suna 'The Conscience" ne da misalin ƙarfe 00:23 na ranar Juma'a.
Ƙungiyar ta yi shirin zuwa Gaza tare da mutane ciki kuma har da ƴar gwagwarmayar nan mai fafutuka kan sauyin yanayi, Greta Thunberg kuma ta ƙalubalanci yaƙin da take yi wanda ba halattacce ba ne da ma hana shigar da kayan jinƙai.
Gwamnatin Malta ta ce duk waɗanda suke cikin jirgin an tabbatar da cewa suna cikin ƙoshin lafiya sannan kuma an kashe wutar da ta kama jirgin.
Ƙungiyar ta yi kira da a kira jakadun Isra'ila domin su bayar da bahasi dangane da 'karya dokokin ƙasa da ƙasa da suka haɗa da hana shigar da kayan agaji Gaza a yanzu da kuma jefa wa jiragenmu na ruwa ba."
Amurka ta ce tana bincike kan rahoton kai harin.
Greta Thunberg ta ce:
"Abin da muka sani shi ne cewa mu masu fafutukar kare haƙƙin ɗan adam za mu ci gaba da duk wani abu wajen ganin mun nemi ƴancin ƙasar Falasɗinu da kuma buɗe hanyar shigar da kayan agaji," in ji ta.
Gwamnatin Malta ta ce akwai matuƙa 12 a cikin jirgin inda ita kuma ƙungiyar ta ce mutum 30 ne a cikin jirgin.
Freedom Flotilla Coalition ta saki wani bidiyo da ke nuna wuta a jirgin. ta ce harin ya nufi injin da ke bai wa jirgin wuta wanda ya bar jirgin ba tare da haske ba sannan kuma cikin haɗarin nutsewa.