Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An bai wa Mbappe jan kati a karon farko a Real Madrid
An bai wa Kylian Mbappe jan kati a karon farko a Real Madrid a karawar da ta doke Alaves 1-0 a wasan mako na 31 a La Liga ranar Lahadi.
Real ta ci ƙwallon ta hannun Eduardo Camavinga tun kan hutu, kuma Alaves ba ta farke ba da kai Real Madrid ta samu maki ukun da take bukata.
Sai dai minti huɗu da Real ta ci ƙwallo ne, sai aka bai wa Kylian Mbappe jan kati kai tsaye, saboda ketar da ya yi wa Antonio Blanco, wadda ta yi muni.
Ƙyaftin ɗin tawagar Faransa, wanda ya ci ƙwallo 22 a La Liga a kakar nan, ya bayar da uku aka zura a raga, ya karbi katin gargadi uku kawo yanzu.
Mbappe ya koma Real Madrid kan fara kakar bana daga Paris St Germain, bayan da kwantiraginsa ya kare da ƙungiyar Faransa.
Karo na biyu a jere da aka bai wa Real jan kati, bayan wanda aka yi wa Eduardo Camavinga a wasa da Arsenal a Champions League ranar Talata a Emirates.
Kenan Camavinga ba zai yi wa Real wasan da za ta fafata da Arsenal ba ranar Talata a Santiago Bernabeu, zagaye na biyu a kwata fainal a Champions League.
A dokar La Liga, idan aka bai wa ɗan wasa jan kati, zai yi hutun fafatawa biyu kenan, kafin daga baya ya buga wa ƙungiyarsa tamaula.
Saboda haka Mbappe ba zai yi wa Real wasan La Liga da Athletic Bilbao da kuma Getafe ba, amma sai mahukuntan gasar La Liga ne za su tabbatar da hakan.
Real Madrid ta samu maki 66, bayan cin Alaves ranar Lahadi, amma tana mataki na biyu da tazarar maki bakwai tsakani da Barcelona mai maki 70, wadda take jan ragama.