Kolo Muani zai tilasta wa Frankfurt ta sayar da shi ga PSG

Asalin hoton, Getty Images
Kolo Muani ya sanar da Eintracht Frankfurt ba zai sake yin atisaye ba, a shirin da yake na tilasta wa kungiyar ta sayar da shi ga Paris St-Germain.
PSG na son sayen dan wasan mai shekara 24, wanda yanzu ya mayar da hankali kan yadda zai koma taka leda a gasar ta Ligue 1.
Kenan dan kwallon tawagar Faransa, ba zai buga wa kungiyar wasan neman gurbin shiga gasar Europa Conference da za ta kara da Levski Sofia ranar Alhamis ba.
Daraktan wasanni na Frankfurt, Markus Kroesche ya fada cewar: "Irin wannan dabiyar ba za ta sa su sayar da shi ga kungiyar Faransa ba.''
Muani yana da kunshin yarjejeniyar da za ta kare a kungiyar ta Jamus zuwa karshen kakar 2027, an kuma ce ya kai darajar yuro miliyan 100.
Dan wasan ya ci kwallo 26 a karawa 50, tun bayan da ya koma Frankfurk daga Nantes.
Muani ya buga wa tawagar Faransa wasa tara har da a gasar cin kofin duniya a 2022 da Qatar ta karbi bakunci.








