Man United ta ci wasa na biyu a Premier League

Man United

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Manchester United ta kawo karshen koma-bayan da take fama da shi na wasannin da take bugawa a waje a Premier, bayan ta sha da kyar a gidan Southampton.

Kocin kungiyar Erik ten Hag ya kara fitowa da ‘yan wasan da ya doke Liverpool da su a ranar Litinin din da ta gabata, domin samun damar gina tawagar mutum 11 da zai rika fara wasanni da ita.

A minti 10 da dawowa daga hutun rabin lokaci ne Bruno Fernandes ya jefa kwallo daya tilo da ta bai wa United nasara a wasa, ta samu maki uku.

Saits, wadda ta tsallake rijiya da baya da kwallon ta tsaya a daya, domin kuwa tun a minti 45 din farko an buga wata kwallo sau uku yan bayan kungiyar nah ana ta shiga, Anthony Elanga ya buga Armel Bella-Kotchap ya tare ta sai kuma Christian Eriksen shi ma.

Dan was an bayan United Diogo Dalot ne ya kwaso kwallon ta sauka a kafar Bruno, shi kuma ya bugata har cikin zare.

A wannan karon ma kyaftin din kungiyar Harry Maguire bai buga wasan ba, kuma bai fara da Ronaldo ba duk da dai ya sanya shi a wasan da wuri ba kamar yadda ya sanya shi a wasan Liverpool ba.

Ten Hag ya sanya sabon dan wasan da ya sayo daga Real Madrid, Casemiro wanda aka saya kan kudi fan miliyan 60.