Me ya sa 'yan Pakistan ke yin kasadar zuwa Turai ta Libya?

    • Marubuci, Caroline Davies
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC a Pakistan
  • An wallafa

Dubban ƴan Pakistan ne ke tafiya Turai ta Libya domin neman aiki.

Suna amfani da kwale-kwale duk da haɗarin da ke tattare da shi a lokacin da wani jirgin ruwa cike maƙil ya nutse a gaɓar tekun Girka a watan Yuni, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da dama.

'Ƴan Pakintan kusan 13,000 da suka tafi Libya da Masar a bana, yawanciinsu ba su dawo ba, ciki har da wasu matasa biyu waɗanda kalmarsu ta ƙarshe ga mahaifiyarsu ita ce, kada ta shiga damuwa babu abin da zai faru da su.

A ofishin 'ƴan sanda da ke lardin Punjab, yanayin zafin wajen ya kai maki 35C a ma'aunin selshiyas, ana ci gaba da fuskantar zafi a yankin, zufa na ci gaba da kwarara a gadon bayan tawagar BBC saboda zafin.

A cikin wannan ƙaramin ɗakin na ofishin 'yan sanda akwai maza 16, suna zaune a kan dandamali, damshi ya yi wa ɗakin yawa. Sai fankar sama da ke juyawa, akwai kuma sanduna a bayan ƙofar ɗakin sai kuma banɗaki guda a cikin ɗakin.

Dukkan waɗannan mutanen ana zargin su ne da hannu wajen safarar mutane, akasarin mutanen da ake zargin suna cikin mutanen da ke cikin jirgin da ya nuste a tekun Girka ranar 14 ga watan Yuni.

Kusan 'ƴan Pakistan 300 ne ake tsammanin ko dai sun nutse a ruwa ko kuma an harbe su. Cikinsu akwai wasu samari biyu, Farhad mai shekaru 15 da Touheed mai shekaru 18.

Wakilan BBC sun tambaye su, ko akwai wanda ke son yin magana. Galibi sun kawar da kai, alamar da ke nuna ba su son yin magana.

Amma sai daga bisani wani ya daka tsalle ya ce zai yi magana, sunan shi Husnain Shah, ya ce wannan ne karo na uku da aka tsare shi. Ya kasance mai safarar mutane tsawon shekara 10, inji shi, ko da yake ya musanta cewa ya taka rawa sosai a hatsarin jirgin ruwa a gabar tekun Girka.

"Ana fama da rashin aikin yi a nan, mutane na zuwa har gidajenmu suna neman mu yi masu hanya su da iyalansu tafiya ƙasashen ƙetare," inji shi.

Ya amince cewa ya yi wa dubban mutanensu hanyar tafiya ƙasashen ƙetare a tsawon lokacin da ya kwashe yana harkar.

"Na shiga harkar safarar mutane saboda babu wata sana'a da nake yi. Ba ni da wata tsayayyar rawa da nake takawa, mutanen da suke zama a Libya masu ƙudi sosai su ne ke amfana da harkar, amma ba na samun ko da kaso 10 na kuɗin da ake biya."

Da aka tambaye shi ko ya yake ji idan ya tuna waɗanda suka rasu ta dalilin hanyar da ya yi masu ta tafiya, sai muryarsa ta sauya.

"Ina jin ba daɗi sosai, mun ji kunya matuƙa kan hakan. Amma ya za mu yi? Idan ma ban yi safarar su ba wani zai yi."

A yayin da tattalin arziƙin ƙasar ke kara taɓarɓarewa, hauhawar farashin kayayyaki ta kai kusan kashi 40 cikin 100, sannan kuma darajar ƙudin Pakistan ta ragu.

Da yawan 'ƴan ƙasar na neman zuwa kasashen waje, inda ko da sun samu albashi mafi ƙaranci, to zai wuce duk wani abu da za su samu idan suka tsaya.

Wani bincike da aka gudanar a karshen shekarar da ta gabata ya nuna cewa kashi 62 cikin 100 na yara maza da matasa masu shekaru 15 zuwa 24 na son barin ƙasar. Yayin da wasu ke tafiya bisa ƙa'ida, wasu kuwa na neman hanyar da za ta fiye masu sauƙi.

Bin ɓauraniyar hanya da ƴan ci rani ke yi na da baƙar wahala, sai dai hukumomin Pakistan sun shaida wa tawagar BBC cewa nutsewar jirgin ruwan Girka na baya-bayanan ya yi ƙarin ya nuna yadda hanyoyin da ƴan ƙasar ke amfani da su wajen tsallakawa ƙasashen ƙetare, inda suke tafiya Dubai daga can su wuce Masar ko Libya, daga nan su shiga babban jirgin ruwa a gabashin Libya zuwa Turai.

A halin yanzu Pakistan na da karancin 'ƴan gudun hijira da ke bin wasu hanyoyin na daban. Mutanen da ke bi ta Iran ba su da yawa tun bayan da ƙasar Turkiyya ta daƙile masu shiga ba bisa ƙa'ida ba, in ji Mohammed Alam Shinwari, wanda ke jagorantar binciken haƙikanin abin da ya faru da jirgin ruwan da ya nutse a Girka.

Ya shaida wa BBC cewa kusan mutum 13,000 ne suka bar Pakistan don zuwa Libya ko Masar a cikin wata shida na farkon shekarar 2023, idan aka kwatanta da kusan 7,000 a 2022. Daga cikin 13,000, 10,000 ba su dawo ba.

"Ba mu sani ba ko har yanzu suna Libya ko kuma sun tafi ƙasashen Turai."

Abin mamaki ne a ce nutsewar jirgin ruwan Girka ne ya ankarar da jami'an ƴan sanda yadda 'ƴan Pakistan ke bin hanyar Libya domin zuwa Turai.

"Mutane ba su kai ƙorafi wajen ƴan sanda, suna zuwa kotu ne kaitsaye, muna shan walaha matuƙa wajen tattara bayanai saboda iyaln waɗanda lamarin ya shafa basason yin magana."

Wani abin da ke ƙara sarƙakiya ga lamarin shi ne yawancin masu tafiya suna amfani da cikakkun takardun bizar Dubai da Masar, saboda haka zai yi wahala a iya dakatar da su.

Hakan na nufin suna kashe maƙudan kuɗaden da suka kai miliyan 2.5 zuwa 3 na kuɗin Pakistan watau Rufi, kwatankwacin dalar Amurka 8,725 zuwa 10,470.

Wannan ne adadin kuɗin da yawansu ke biya domin tsallakawa ƙasashen ƙetare.

Yawancin waɗanda suka yi nasarar tsallakawa, sun maƙale a Libya.

Tawagar BBC ta tsaya a wani ƙauye da ke Punjab domin tattaunawa da wasu daga cikin iyalan waɗanda suka maƙale a Libyar, sai dai ko da suka tsaya sai mutanen ƙauyen suka baibaiye su.

Da yawan matasan ƙauyen sun tsallaka zuwa Libya sai dai har yanzu suna can, suna kuma aiko wa ƴan uwansu da saƙon muryoyi da faifan bidyonsu domin roƙonsu kuɗade.

Lamarin akwai rikitarwa, saboda iyalan ba su sani ba ko ƴan uwan nasu na hannun masu safarar ne ko kuma hukomomin Libya ne suka tsare da su, ko ma wani daban.

Sai dai iyalan sun roƙi BBC da kada ta bayyana bayanan su saboda waɗanda ke riƙe da ƴan uwan nasu za su iya ɗaukar mataki kan mutanen da suke tsare da su.

Wani uba ya ce: "Suna ba su abinci sau guda a cikin kwana biyu zuwa uku."

Ma'aikatar harkokin waje ta Pakistan ta ce suna sane da abin da ke faruwa kuma suna aiki kan hakan.

Duk da tarin matsalolin da ke tattare da tsallakawa ba bisa ƙa'ida ba, BBC ta tattauna da mutane masu yawa da suka ce yanzu haka suna neman hanyar da za su tsallaka ta haramtacciyar hanya.

Ɗaya daga cikin masu safarar mutane mazaunin Turai ya shaida wa BBC cewa har yanzu hanyoyin da suke amfani da su wajen safarar mutane a buɗe suke kuma suna ci gaba da fitar da 'ƴan Pakistan zuwa Turai. Kuma ƴan sanda ma sun tabbatar da cewa sun san mutane na ci gaba da barin ƙasar ba bisa ƙa'ida ba.

Da yawan mutanen da BBC ta tattauna da su, imma sun taɓa zuwa ko kuma suna son zuwa ko su tura 'ƴa'ƴansu, dukkansu suna da ƙwarin gwiwar samun makoma mai kyau.