'Yan matan Colombia sun doke na Jamaica a gasar Kofin Duniya

An wallafa

Colombia za ta buga wasan daf da na kusa da na karshe a gasar Kofin Duniya ta Mata da Ingila bayan da ta doke Jamaica da ci 1-0, a wasan zagaye na biyu da aka buga a filin wasa na Melbourne.

Kyaftin din Colombia Catalina Usme ce ta zira kwallon a raga a minti na 51 da fara wasa.

Ita ce kwallo ta farko da aka ci Jamaica a gasar cikin mintuna 321 da ta buga.

Wannan ne karon farko da Colombia ta kai zagayen kwata fayinal a gasar ta mata.

Za su kara da zakarun Turai Ingila a filin wasa na Australiyaa da ke Sydney ranar Asabar 12 ga watan Augusta.