Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko masu dalilin aure za su iya rage yawan maza tazurai a China?
- Marubuci, Helen Bushby
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Culture reporter at Sheffield Documentary Festival
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Cewa maza sun zarce mata yawa da tazara mai nisa a China ba sabon labari ba ne.
Saboda tazarar miliyan 30 da ke tsakanin yawan mata da maza, ƙasar da ta fi kowacce yawan al'umma a duniya ta faɗa cikin yanayin ƙarancin mata da mazan za su yi soyayya da su ko kuma aure.
Mazan China da dama suna rayuwa cikin yanayi na takura da matsin lamba saboda sun gaza ƙulla soyayya ko aure da wata.
Wani ƙwararre a kan koyar da soyayya mai suna Hao, wanda ke da mutane fiye da dubu uku da ke ɗaukar darasi a wajen shi ya ce ƙarin matsala ma ita ce idan namiji ya fito a gidan talakawa ko masu ƙaramin ƙarfi domin kuwa hakan na yin tasiri wajen samun wadda za ta yarda su ƙulla soyayya.
"Mafi yawan su ƴan ƙwadago ne, domin haka suna shan wahala kafin su samu mata,'' in ji Hao.
Mun shaida irin yaddda abin ke gudana a cikin fim ɗin Violet Du Feng, inda aka nuna rayuwar Hao da wasu matasa uku masu ɗaukar darasi a wajen shi, game da yadda za su iya samun matan aure, a cikin horon da ya yi masu na tsawon mako guda.
Daga su har Hao duk ƴaƴan talakawa ne, kuma sun tsinci kansu a cikin mutanen da suka yi yarinta a farkon shekarar 1990, lokacin da iyaye da dama ke barin ƙananan ƴaƴansu a wajen wasu ƴan uwa, yayin da su kuma suke tafiya birane domin yin aiki.
Waɗan nan yara dai a yanzu sun giram, kuma su ma su na shiga birane domin ƙoƙarin neman matan da za su aura da kuma neman arziki.
Du Feng, wadda ke zaune a Amurka ta na so fim ɗinta ya bayyana irin rayuwar da matasa ke fuskanta a ƙasar ta.
Ta shaidawa BBC cewa "Ina ganin a wannan lokaci da babu daidaito tsakanin yawan mata da kuma maza, abin da ya fi dacewa shi ne zaƙulo hanyar ɗinke wannan ɓaraka,''
Daluban Hao uku, Li mai shekara 24, da Wu mai shekara 27 da kuma Zhou mai shekara 36, duk suna ƙoƙari ne na saita rayuwar su bayan tsarin gwamnati na ƙayyade haihuwa ɗaya kacal ga ƴan China.
Gwamnatin China ce ta ɓullo da tsarin a1980 lokacin da yawan mutanen ƙasar ya doshi biliyan ɗaya, inda aka yi hasashen ci gaba da haihuwa babu wata doka da ke sanya ido zai iya shafar bunƙasar tattalin arzikin ƙasar.
Amma saboda al'adar fifita son haihuwar namiji a kan mace, sai aka riƙa watsar da jarirai mata bayan an haifesu, ko a kai su gidan kula da marayu ko kuma a zubar da cikin bayan gano cewa mata ne ake ɗauke da su, lamarin da zama ruwan dare har ya kai China ga halin da take ciki na gagarumin giɓi tsakanin yawan maza da na mata.
A 2016 China ta canza wannan tsari, bayan fargabar da ta taso kan yadda tsofaffi suka yawaita , kuma wasun su babu aure balle haihuwa. Saboda haka ne a yanzu ake shirya taro domin haɗa aure daga lokaci zuwa lokaci.
Wu da Li da kuma Zhou suna so Hao ya taimaka masu su samu ƴanmata a wajen taron.
Suna fatan zama kamar Hao, kasancewar shi ma ya yi nasarar samun mata mai suna Wen, wadda itama ƙwararriya ce a harkar koyar da soyayya da aure.
Hao yana koya masu kwalliya da dabarun iya soyayya da kuma yadda za su ja hankalin ƴanmata zuwa gare su. Kuma suna ɗaukar darasin ne kodai ta kafar intanet ko kuma ido da ido.
Sai dai duk da ƙoƙarin nasu ba komai ke tafiya yadda aka tsara ba.
Hao yana amfani da salon zance wajen kwatance mazan da ya ke tallatawa, kuma a wasu lokutan yana ƙara gishiri a kwatancen nasa, lamarin da Zhou ke ganin an shigar da ƙarya a ciki.
Ya ce "Ina ji ban kyauta ba saboda ina sane aka yaudari mutane ta hanyar bayyana masu abin da na san ba gaskiya bane a kaina.''
Du Feng dai tana ganin cewa matsalar ta duniya ce baki ɗaya ba China kaɗai ba.
Ta ce "Tabbas haka abin yake a China, amma fa a duniya baki ɗaya ma haka abin yake. Muna faɗi-tashin daidaita rayuwar zahiri da abin da muke tallatawa a kafafen sadarwa. A halin da ake ciki abu ne mai wuya a fayyace tsagwaron gaskiya a intanet, musamman a harka irin ta tallata mazan da ke neman soyayya ta wannan hanya.''
Hao na daga cikin mutanen da suka yi fice a China, cikin sana'arsu ta dalilin aure, amma mun shaida yadda matarsa ke nuna shakku a kan wasu dabarun da yake amfani da su.
Daga cikin su akwai yadda ya ke sanya maza su feshe hammatarsu da turare kafin zuwa ganawa da mata da ya haɗa su, kuma sau tari ana haɗuwa ne a cikin yanayin da matan ba zasu samu damar tantance abin da suke fatan tantancewa a rayuwar mazan da aka haɗa su ba.
Dr Zheng Mu, daga jami'ar Singapore ta shaidawa BBC yadda matsin-lamba kan rashin aure ke iya damun rayuwar maza tazurai.
Ta ce "A China, ana bayar da muhimmanci sosai ga buƙatar namiji ya yi aure kuma ya zamo magidanci mai sauke duk nauyin da ke kansa na aure,''
"Saboda haka suna faɗawa cikin damuwa idan aka ce namiji ya kasa samun macen da za ta amince ta aure shi, ta yadda har abin yana shafar lafiyar ƙwaƙwalwar wasu a cikin mazan.'' in ji ta.
Zhou ya damu tsadar halin da yake ciki, na kashe maƙudan kuɗi domin neman wadda zai aura, ga sallamar mai dalilin aure, ga kashe kuɗin sayen abincin da suke ci da wadda aka haɗa su, ga kuma takurar sayen sabbin kaya domin fitowa fes-fes.
"Ina samun $600 (£440) a kowanne wata, amma haɗuwa ɗaya kacal da macen da aka haɗamu ina kashe $300.'' in ji Zhou.
Ya ƙara da cewa a ƙarshe dai dole mu yarda cewa al'umma ce ke ƙayyade mana yadda za mu rayu"
Du Feng ta yi bayanin cewa: "Muna rayuwa ne a cikin wata al'umma da ake daraja maza ko akashin hakan saboda dukiyar da suka tara.''
Fim ɗin bai taɓo halin da rayuwar maza ƴan luwaɗi take a China ba.
Du Feng ta haƙiƙance cewa cal'ummar China ba ta amince da harkar ƴan luwaɗi da ƴan daudu ba, yayin da Dr Mu ke cewa : "A China, aure alaƙa ce ta mace da namiji kuma haka doka ta sani.''
"To saboda haka ana sa ran namiji ya auri mace ne kaɗai domin cika sharaɗin al'ada.'' in ji Dr Mu.
Fim ɗin ya kuma nuna yadda fasahar zamani ta karkatar da yanayin soyayya zuwa wadda ake yi ta intanet, inda aka nuna cewa mata fiye da miliyan 10 ke soyayya ta intanet a China.
A shekarar da ta gabata, Kafar Reuters ta ruwaito cewa ana ƙara samun maza tazurai a China.
"Ina damuwa sosai a game da yadda rayuwar soyayyar mu ta canza sosai a wannan zamanin, musamman a tsakanin matasa,'' in ji Du Feng.
Ta ƙara da cewa "Fim ɗina ya mayar da hankali ne a kan yadda muka koma rayuwar kaɗaici, inda dukkan mu muke neman hanyar da za mu haɗu da masoya.
A ƙarshen fim ɗin, mun ga yadda maza da dama ke faɗi-tashin neman yadda za su cimma nasara a matsayinsu na maza, da yadda za su samu karɓuwa a cikin al'umma, cikin su harda Hao.
Shi kuma Hao, ya gamsu cewa ''Idan har ka ƙaunaci kanka, to babu shakka za ka samu ƴanmatan da za su soka.''