Hyda: Balarabiyar da ke horar da matasan Kano ƙwallon ƙafa

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Hyda Ahmad Ghaddar mai shekaru 27 da haihuwa kociya ce da horar da matasa ƙwallon ƙafa a ƙungiyarta mai suna 'Breakthrough Football Academy'.

Matashiyar ta fara buga ƙwallo ne tun tana ƴar shekara shida da haihuwa tare da ƴan uwanta a ƙofar gida.

An haifi Hyda a Lebanon amma iyayenta sun koma birnin Kano a lokacin da take ƴar watanni biyu, inda ta shafe shekara 16 a Kano kafin daga baya ta sake komawa Lebanon ɗin bayan kammala karatun jami'a.

A ƙasar tata ta asali wato Lebanon ne Hyda ta tsunduma harkar wasan ƙwallon ƙafa gadan-gadan, inda har ta shiga makarantu na samun horo a fannin kociya a ƙwallon ƙafa a Lebanon da Burtaniya.

Ta buga ƙwallo ƙafa a Najeriya da Spain da Burtaniya da kuma Lebanon.

Sai dai kuma Hyda ta so yin ƙwallo ƙafa a matsayin ƙwararriyar ƴar ƙwallo amma kuma sakamakon rauni da ta samu ya sa sauya tunaninta zuwa mai horas da ƴan ƙwallon ƙafa.

Ta yi digirinta na farko a fannin kimiyyar motsa jiki da kiwon lafiya wato PHE sannan ta yi digiri na biyu sannan ta yi kwasa-kwasai a fannin kociya har ma ta yi karatun bayar da horo ga masu son zama kociya.

Tana kuma da lasisi daban-daban kan horas da ƴan ƙwallo.

'Ina so na ga Kanawa a manyan kulob'

Hyda ta buɗe ƙungiyar ƙwallon ƙafar ta 'Breakthrough Football Academy' a Kano watanni shida da suka gabata inda take da burin bai wa Kanawa dama su shiga duniyar wasanni.

"Na zama kociya ne saboda tunanin da nake da shi na taimakon al'ummar Kano bisa la'akari da irin taimakon da al'ummar Kano suka yi mini.

"Babban burina shi ne samun wasu daga cikin waɗanda nake bai wa horo sun yi fice a duniyar ƙwallo." In ji Hyda Ahmad.

Ta kuma ƙara da cewa wani ƙarin burin nata shi ne a samu babbar ƙungiyar wasa ta mata zalla a Kano "domin a Kano akwai matan da suka iya ƙwallon ƙafa amma saboda rashin dama ba a jin su."

Ƙungiyar tata mai suna 'Breakthrough Football Academy' na gayyato ƴan wasa kuma "idan mun ga mutum ya yi mana sai mu riƙe shi idan kuma bai dace ba sai mu ba shi haƙuri."

Hyda Ahmad Ghaddar ta yi wasan ƙwallon ƙafa inda kuma ta fi taka ƴar wasan tsakiya.

Hyda ta ce ta samu ƙwarin gwiwa daga iyalinta tun daga farko kasancewarsu maso son ƙwallon ƙafa.

Daga ƙarshe Hyda ta ce ita ƴar AC Millan ce.