Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea ta ɗauki Wiley daga Atalanta
Chelsea ta amince da farashin £8.5m, ƙudin sayen ɗan ƙwallon Amurka, mai tsaron baya, Caleb Wiley daga Atlanta United.
Mai shekara 19 zai saka hannu kan yarjejeniyar kaka bakwai a ƙungiyar Stamford Bridge daga nan a bayar da aronsa ga Strasbourg ta Faransa, ɗaya daga mallakin rukunin BlueCo.
Sai dai makomarsa na Chelsea, wadda take ganin zai zama fitatcen ɗan ƙwallon kafa a duniya nan gaba.
Wiley ya yi wa Amurka wasa biyu, yana cikin waɗan da za su wakilci kasar a gasar tamaula a Olympics da birnin Paris zai karɓi bakunci a bana.
Chelsea ta yi nisa wajen cinikin Aaron Anselmino daga Boca Juniors, sannan ta kusan kammala sayen ɗan wasan Basel, Renato Veiga.