Real ta doke Celta Vigo, ta ƙara matsa wa Barca lamba

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kylian Mbappe ya ci kwallaye biyu a wasan da Real Madrid ta doke Celta Vigo da ci 3-2 a filin wasa na Santiago Bernabeu.

Real ta fara cin kwallo a minti na 33 ta hannun Arda Guler - sannan bayan minti shida Mbappe ya zura ta biyu, inda ya ɗaɗa kwallon daga wajen yadi na 18 har cikin raga.

Ɗan wasan ɗan asalin Faransa ya ci ta biyu minti uku bayan komawa daga hutun rabin lokaci, inda ya karɓi kwallo daga hannun Guler - inda ya yi amfani da kafarsa ta hagu wajen zura ta a raga.

Sai dai Celta ta farke ta hannun Javi Rodriguez a minti na 69, bayan bugun kusurwa.

Ba a jima ba Williot Swedberg ya ci ta biyu inda wasa ya koma 3-2 a minti na 76.

Haka kuma Celta ta yi ta kai kora har alkalin wasa ya busa tashi.

Yanzu dai Barca ta bai wa Madrid tazarar maki huɗu - inda za su fafata a wasan El-clasico a mako mai zuwa.

Wasa ne kuma mai muhimmanci ga duka ƙungiyoyin da ke ƙoƙarin lashe gasar Laliga.