Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Za a ɗauki lokaci mai tsawo wajen sake gina Gaza'
- Marubuci, Paul Adams
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC diplomatic correspondent
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Da waɗanda suke ƙasa, da waɗanda suke mota, yanzu tafiyar komawa gida ta fara.
Ga ƴan Gaza da aka raba da gidanjensu a cikin watanni 15, tafiyar ba mai nisa ba ce- zirin Gaza wani ɗan ƙaramin guri ne- sai dai tafiyar ta yau na nuna farkon makoma mara tabbas ga yankin da yaƙi ya ɓarnata.
''Babu wutar lantarki, ba ruwa, babu kayayyakin more rayuwa,'' a cewar ƴar jarida a Gaza Ghada el-Kurd, a lokacin da take shirye-hiryen na komawa arewaci daga Deir el-balah, inda ta ke tsugune na tsawon watanni.
'' Dole mu fara komai tun daga farko.''
An fara biyan buƙatun da suka fi muhimmanci, wato abinci da wurin zama.
'' Ana samun shigowar kayyakin agaji fiye da yadda muke gani tun da aka soma yaƙin,'' inji Sam Rose, jami'i a hukumar jin-ƙai na Falasɗinawa na Majalisar Ɗinkin Duniya.
''Sakamakon hakan, muna iya samar da abubuwa da aka fi buƙata kamar abinci, da ruwa, da barguna, da kuma abubuwan kula da tsafta. Amma bayan haka, akwai babban aiki a gaba.''
Samun mafaka a cikin kangon da Gaza ya zama, zai kasance matsala ta farko cikin manyan matsalolin da za a fuskanta nan gaba.
Aƙalla mutum 700,000 ne suka tsere daga birnin gaza da yakunan da ke kewaye da shi a makonnin farkon yaƙin. Sai kuma adadin da ba'a sani ba, da ake hasashen sun kai 400,000 da suka cigaba da zama a birnin.
Wasu daga cikin yankunan an lalata su baki-ɗaya, sannan wasu kuma da ƙyar suka tsira.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi hasashen cewa an lalata ko ruguza aƙalla kashi 70 cikin ɗari na gidajen da ke zirin Gaza tun watan Oktoban 2023, kuma lamarin ya fi ta'azzara a arewaci.
Birnin Jabaliya, wanda ke da mutane 200,000 gabanin fara yaƙin, kusan rabinsu su koma rayuwa a sansanin ƴan gudun hijira mafi girma da daɗewa a Gaza, amma an lalata shi baki ɗaya.
Ofishin yaɗa labarai na gwamnatin Gaza da Hamas ke iko da shi, ya yi kiran buƙatarsu ta gaggawa da a samar musu da rumfuna da motocin da ake iya kwana a cikinsu guda 135,000.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce a yanzu ta samu nasarar shigowa da runfuna 20,000 waɗanda suka maƙale a kan iyaka tun watan Agusta, tare da adadi mai yawa na kaya da ke hana ruwa shiga da kuma katifu.
Sai da majalisar da ce za ta yi fama wajen cimma buƙatar da ake da shi na rumfuna.
'' A taƙaice dai babu rumfuna da yawa a ko ina a duniya da aka ƙera su domin ayyukan ceto,'' inji Mista Rose.
Mutanen da suka yi ƙoƙarin zama a arewaci har tsawon lokacin da ake yaƙin na fargabar tsaikon da za a samu a neman gurin zama, wanda ko a yanzu ya yi tsanani.
''Akwai babbar matsala saboda a baya mutane na zama a gidajen ƴan'uwa ko abokai da ke kudanci,'' A cewar Asmaa Tayeh, wadda iyalinta suka tsere daga Jabaliya amma ba su bar arewaci ba.
''A yanzu dole su fice daga waɗannan gidanjen su baiwa masu shi, saboda haka, za a shiga wani sabon yanayi na rasa muhalli.''
Asmaa ta ce a yanzu haka iyalai huɗu ke zama a gidanta, kuma ana sa ran ƙarin wasu uku nan gaba. Rashin isashen wuri da kuma rashin sirri, a cewar ta, ya fara kaiwa ga zaman ɗarɗar.
Dawowar na ƴan gudun hijira na kuma da wasu tasirin.
''Na je kasuwa a yau in saya kifi,'' inji Asmaa."' Amma har masu sayarwar sun fara ƙara farashi.''
Takurar da ake da ita kan ruwa da wutar lantarki da ba su da wadata ba a yanzu zai iya ƙaruwa.
Amma a dukkan waɗannan hasashen da ake yi na wahalhalun da za a iya fuskanta, waɗanda suke dawowa suna magana, kan sauƙin da za su samu da abin da suke sa rai.
''Muna cikin farin ciki mara misaltuwa da dawowarmu arewaci, inda za mu iya samun natsuwa,'' wata mata ta shaidawa BBC.
A cewar waɗanda suka ga Beit Hanoun a baya bayan nan - da ke can yankin arewa masu gabashi mafi nisa na zirin Gaza, kusa da iyakarta da Israila- yanzu ba sa iya gane garinsu.
To amma me ake ciki game da shawarar Donald Trump na cewa mutane su koma, ko na wucin gadi ko na dindindin zuwa Masar ko Jordan?
Hukumomi a Masar da Jordan tuni suka yi watsi da shawarar.
Ƙasashen biyu na tsoron tasirin tsaro da shigowar gaggawa na ƴan gudun hijira masu cike da fargaba da ruɗani zai samar.
Ƙasar Jordan na ƴan Jordan ne, kuma Falasɗin na ƴan Falasɗinu ne,'' a cewar ministan harkokin ƙasashen wajen Jordan, Ayman Safadi.
A yanzu haka ƙasarsa na ɗauke da ƴan gudun hijirar Falasɗinu miliyan 2.4 waɗanda aka musu rijista.
Shawarar Shugaba Trump ta samu karɓuwa a tsakanin ƴan majalisu masu tsattsaurar ra'ayi da ke majalisar ministocin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
Ministan kuɗi, Bezalel Smotrich wanda yake goyon bayan Israila ta ƙwace zirin Gaza, ya ce '' shawara ce mai kyau.''
Da yake magana a wani taron magoya baya a bara, ya yi magana kan ƙirƙiro yanayin da zai sa a rage adadin mutanen da ke Gaza zuwa rabin yadda suke a yanzu cikin shekaru biyu.
Sai dai idan an yi gaggawar gina Gaza, kuma ƴan ƙasar sun fara samun makoma mai kyau, Smotrich zai iya samun yadda yake so.
''Ina ganin a watannin farko, za su ga abin da zai faru,'' a cewar ƴar jarida Ghada el-Kurd.
''Idan suka rasa komai, kuma aka samu jinkiri wajen sake gina yankin, ina ganin mutane ba za su zauna a Gaza ba.''
Aƙalla mutane 150,000 sun riga sun fice tun fara yaƙin a Oktoban 2023.
Ghada ta ce tana ganin cewa wasu mutanen da ba za su iya cigaba da zama ba, za su bi su, su nemi mamora a ƙasashen Larabawa ko gaba da nan, sannan za a bar talakawan da marasa galihu a baya.
''Na yarda da maganan Trump na cewa mutane sun cancanci rayuwa mai kyau,'' inji ta. '' Amma me ya sa ba a Gaza ba?''