De Gea ya sha dan karen yabo a wajen Erik ten Hag

An wallafa

Kociyan Manchester United, Erik ten Hag ya yabi mai tsaron raga, David de Gea kan rawar da ya taka a wasan Premier da West Ham.

Ranar Lahadi United ta ci West Ham 1-0 a wasan mako na 14 a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Marcus Rashford ne ya ci kwallo kuma na 100 a kungiyar ya zama na 22 a United da suka yi wannan bajintar, na farko tun bayan Rooney a 2019.

Ten Hag ya ce De Gea fitatcen dan wasa ne, ya kara da cewar dan kwallon ya dace ya wakilci Sifaniya a gasar kofin duniya a Qatar.

Za a fara gasar kofin duniya a Qatar ranar 20 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan Disambar 2022.

Wasu rahotanni na cewar De Gea baya kan ganiya da zai iya tsare ragar Sifaniya, shi ya sa baya cikin 'yan kwallo 55 da aka bayyana a kasar kafin babbar gasar na kwarya-kwarya.

Golan wanda shi ne gwarzon United a kaka hudu har da wadda ta wuce mai shekara 31 zai ci karo da koma baya, ida har kasar ba ta gayyace shi kofin duniya ba.

Tuni wasu matasan masu tsaron raga da ke Premier League suka nuna sun shirya maye gurbin De Gea kan rawar da suke takawa a kakar nan.

Masu tsaron ragar sun hada da Robert Sanchez na Brighton da na Brentford, David Raya da kuma Kepa Arrizabalaga, wanda ya koma kan ganiya a wasannin Chelsea.

De Gea ya taka rawar gani a karawa da West Ham ranar Lahadi, wanda ya hana kwallo uku shiga raga da ta Michail Antonio da Kurt Zouma da kuma ta Declan Rice.

Ten Hag ya ce ''Kowa zai iya fadar ra'ayinsa - abu na farko ga kwazon mai tsaron raga shi ne hana kwallo ya shiga ragarsa - De Gea na yin kokari yadda ya kamata.''

De Gea ya zama kan gaba a karbar albashi mai tsoka a United lokacin da ya saka hannu kan kwantiragin fam 375,000 a duk mako a 2019.

United ta koma mataki na biyar a kan teburin Premier da maki 23 ta yi kasa da Chelsea zuwa ta shida mai kai 21.