An yi waje da Italiya a Euro 2024 mai rike da kofin 2020

An wallafa

Italiya ta yi ban kwana da gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2024 da ake buga wa a Jamus, bayan da Switzerland ta doke ta 2-0 a zagaye na biyu ranar Asabar.

Switzerland ta fara cin ƙwallo ta hannun Remo Freuler a minti na 37 da take leda a filin wasa na Olympiastadion da ke Jamus.

Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Switzerland ta kara na biyu ta hannun Ruben Vargas.

Italiya mai Euro biyu da ta ɗauka a 1968 da kuma 2020 ta kai zagayen ƙungiyoyi 16 a Euro 2024, bayan da ta yi ta biyu a rukuni na biyu da maki hudu - Sifaniya ce ta daya da maki tara.

Ita kuwa Switzerland, wadda ba ta taɓa lashe Euro ba, ta kai quarter finals a bana, bayan da ta yi ta biyu a rukunin farko da maki biyar - Jamus ce ta daya da maki bakwai.

Ɗan kasar Poland, Szymon Marciniak ne ya busa wasan, wanda yake da ƙwarewa a jan ragamar manyan fafatawar tamaula.

Shi ne ya yi rafli a wasan karshe a gasar cin kofin duniya a 2022 a Qatar, wanda Argentina ta lashe kofin, bayan nasara a kan Faransa a bugun fenariti.

Haka kuma shi ne ya busa wasan karshe a lokacin da Manchester City ta lashe Champions League a karon farko da ta doke Inter Milan.

Shi ne dai ya busa karawa tsakanin Belgium da Romania a gasar ta Euro 2024 a Jamus a bana.

Wasu batutuwan da suka shafi wasa tsakanin Italiya da Switzerland

Wannan shi ne karo na biyar da aka kece raini tsakanin tawagogin biyu a babbar gasar tamaula a duniya.

Switzerland ce ta yi nasara a gasar kofin duniya a 1954 da cin 2-1 a karawar cikin rukuni da karawar cike gurbi da cin 4-1.

Italiya kuwa ta yi nasara a kan Switzerland da cin 3-0 a karawar cikin rukuni a gasar kofin duniya a 1962 da kuma a Euro 2020.

Tun bayan da Switzerland ta doke Italiya 1-0 a watan Mayun 1993 a wasan neman shiga gasar kofin duniya, tawagar ta yi karawa 11 ba tare da cin Italiya ba a dukkan fafatawa da canjaras shida da rashin nasara biyar.