Mahama ya sha rantsuwar kama aiki a Ghana

Asalin hoton, Manuel Photography
An rantsar da John Dramani Mahama a matsayin sabon shugaban ƙasar Ghana a wani ƙayataccen biki da aka gudanar a dandalin Black Star da Accra, babban birnin ƙasar.
Wannan ya biyo bayan gagarumar nasarar da ya samu a zaɓen shugaban ƙasar na watan Disamban 2024.
Kuma, wannan ne karon farko da ƙasar za ta samu mataimakiyar shugaban ƙasa, mace, Farfesa Jane Nana Opoku Agyemang.
A yau ɗin kuma an rantsar da shugabannin da kuma ƴan majalisar dokokin ƙasar.
Mahama ya taɓa mulkar ƙasar a matsayin shugaba daga shekarar 2012 zuwa 2017.
Shugabannin ƙasashe 21, ciki har da shugaban Najeriya da Ecowas, Bola Tinubu ne suka halarci bikin rantsarwar.
Ya lashe zaɓen ne da kashi 56.55 na ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen, inda ya kayar da Mataimakin Shugaban Ƙasa Mahamudu Bawumia na jam'iyyar NPP mai mulki.
Ƙasar Ghana dai na cikin yanayin matsin tattalin arziƙi inda a yanzu haka take da nauyin bashin da ya kai dalar Amurka biliyan 51.67, baya ga rashin aikin yi da kuma rashawa da cin hanci da suka yi wa ƙasar kakatutu.
John Dramani Mahma ya yi alkawarin dawo da martabar tattalin arzikin kasar ne ta hanyar tabbatar da gaskiya da rikon amana a kashe kudaden gwamnati da kuma yi wa babban bankin Ghana garanbawul.
To sai dai manufar da John Dramani Mahama ya fi shahara da ita ita ce ta tattalin arziki mai tafiya babu ƙaƙƙautawa ba da ake kira '24 hour economic policy' mai cike da taƙaddama.
"A duk lokacin da na yi magana kan tsarin tattalin arziƙi mai tafiya babu ƙaƙƙautawa, akwai bukatar fahimtar dalilin wannan ƙudiri, za mu samar da tattalin arzikin da zai samar mana da abinci da abin sha da magani da tufafin da muke buƙata ta yadda za mu magance matsalar hauhawar kuɗaɗen kasashen waje sakamakon shigo da kayan da ba a bukatar su." In ji Mahma.
Dangane kuma da yaki da rashawa da cin hanci, John Dramani Mahma ya ce zai bai wa hukumomi masu yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa cikakken 'yancin gudanar da ayyukansu.
Ya kuma ya sha alwashin yi wa kundin tsarin mulkin garambawul wajen rage kuɗaɗen da ake bai wa shugabanni da rage yawan masu muƙamin siyasa da kuma samar da daidaito a albashin dukkanin ma'aikatan gwamnati.

Asalin hoton, Getty Images











