Manyan wasannin da ke gaban Man United a shekarar 2025

Asalin hoton, Getty Images
Ranar Laraba za ta kasance 1 ga watan Janairun 2025, za kuma a ci gaba da wasannin kakar bana.
Manchester United wadda ke fatan komawa kan ganiya, za ta buga manyan wasanni a shekarar.
United za ta je Anfield, domin fuskantar Liverpool a Premier League ranar 5 ga watan Janairu ɗaya daga babban wasa da za ta yi a farkon shekarar nan.
Ranar Litinin United ta yi rashin nasara 2-0 a Old Trafford a hannun Newcastle United a Premier League, karo na huɗu da aka doke United a jere.
Ƙungiyar da Ruben Amorin ke jan ragama ta yi kasa zuwa mataki na 14 a kasan teburin Premier, bayan kammala karawar mako na 19.
Ga jerin manyan wasannin da United za ta buga a 2025:
WATAN JANAIRU
1 — Za a buɗe kasuwar saye da sayar da ƴan ƙwallo a Turai
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
11/12 — FA Cup zagaye na uku
30 — Za a kammala wasannin zagayen farko a Europa League
31 —Za a raba jadawalin Europa League wasannin cike gurbi
WATAN FABRAIRU
3 — Za a rufe kasuwar saye da sayar da ƴan ƙwalllon kafar Turai
6 — Karo na 67 da za a yi taron tuna hatsarin jirgin sama da ya rutsa da Manchester United da ake kira Munich Air Disaster da za a yi a Old Trafford da kuma Munich.
8 — Ranar da za a buga FA Cup zagaye na huɗu
13 & 20 — Za a ci gaba da wasannin Europa League
21 — Ranar da za a raba jadawalin Europa League zagayen ƴan 16 da na kwata fainal da karawar daf da karshe
WATAN MARIS
1 — Wasan FA Cup zagaye na biyar
6 & 13 — Zagayen ƴan 16 a Europa League
17-25 — Wasannin kasa da kasa da Fifa kan wware da ake kira international break
29 — Zagayen kwata fainal a FA Cup
WATAN AFIRILU
10 & 17 — Europa Leaguekwata fainal
26 — Wasan FA Cup karawar daf da karshe
MAY
1 & 8 May — Europa Leaguzagayen daf da karshe
17 — Wasan karshe a FA Cup
21 — Wasan karshe a UEFA Europa League a Bilbao a Sifaniya
WATAN YUNI
2-10 — Wasannin kasa da kasa da Fifa kan wware da ake kira international break
WATAN YULI
WATAN AGUSTA
16 — Premier League season begins
WATAN SATUMBA
1-9 — Wasannin kasa da kasa da Fifa kan wware da ake kira international break
WATAN OKTOBA
6-14 — Wasannin kasa da kasa da Fifa kan wware da ake kira international break
NUWAMBA
10-18 — Wasannin kasa da kasa da Fifa kan wware da ake kira international break
WATAN DISAMBA
21 December 2025-18 January 2026 — 2025 Gasar kofin Afirka
Andre Onana (Kamaru), Amad (Ivory Coast) da Noussair Mazraoui (Morocco) za su je wakiltar kasashensu a gasar cin kofin nahiyar Afirka.












