Gudun famfalaƙi da kayayyakin tarihi cikin hotunan Afirka

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Wasu daga cikin zaɓaɓɓun hotunan Afirka da na ƴan nahiyar a wasu sassan duniya cikin makon da ya gabata.

Bikin kayayyakin tarihi da al'adun ƙasar Libiya

Asalin hoton, ESAM OMRAN AL-FETORI / REUTERS

Bayanan hoto, A ranar Juma'a ne aka ƙaddamar da bikin kayayyakin tarihi da al'adun ƙasar Libiya
Angelo Djessan a bikin zane-zane na Graff Ivoire a Ivory Coast

Asalin hoton, LEGNAN KOULA / EPA

Bayanan hoto, Angelo Djessan yana aiki kan wani zanen bango a bikin zane-zane na Graff Ivoire a Ivory Coast ranar Litinin.
Matasa suna buga ƙwallon ƙafa

Asalin hoton, SIPHIWE SIBEKO / REUTERS

Bayanan hoto, Matasa suna buga ƙwallon ƙafa a bakin teku a Mozambiique
Magoya bayan jam'iyyar Pastef da ke mulkin ƙasar Senegal a wani gangamin siyasa

Asalin hoton, ZOHRA BENSEMRA / REUTERS

Bayanan hoto, Magoya bayan jam'iyyar Pastef da ke mulkin Senegal a wani gangami a unguwar Guediawaye da ke birnin Dakar, gabannin zaɓen ƴan majalisar dokokin ƙasar, wanda shugaba Bassirou Diomaye Faye ya kira bayan ya rusa majalisar dokokin ƙasar.
shugaban ƙasar Botswana

Asalin hoton, THALEFANG CHARLES / REUTERS

Bayanan hoto, Bikin rantsar da sabon shugaban ƙasar Botswana Duma Boko a babban birnin ƙasar Gaborone.
Magoya bayan jam’iyyar Kulmiye da ke mulki a jamhuriyar Somaliland

Asalin hoton, LUIS TATO / AFP

Bayanan hoto, Magoya bayan jam’iyyar Kulmiye da ke mulki a jamhuriyar Somaliland mai cin gashin kanta, sun fito gangamin siyasa.
Gasar gudun famfalaƙin mata a birnin Lagos

Asalin hoton, ADEKUNLE AJAYI / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, An ƙaddamar da gasar gudun famfalaƙin mata a birnin Lagos, Najeriya ranar Asabar
Ƴar damben boksin na ƙasar Algeria Imane Khelif

Asalin hoton, MARCO RAVAGLU / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Ƴar damben boksin ta ƙasar Algeria Imane Khelif tana raha da ani mai gabatar da shirye-shirye ɗan ƙasar Italiya a birnin Roma ranar Litinin
Bikin Al'adu a kudu maso yammacin Benghazi

Asalin hoton, MOHAMMED HAMOUD / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Ana gudanar da bikin ne a kudu maso yammacin Benghazi, kuma masu shirya shi na fatan zai zama abin da za ci gaba da yi kowace shekara.
Mabiya ƙungiyar musulmi ta Baye Fall a Senegal

Asalin hoton, JOHN WESSELS / AFP

Bayanan hoto, A ranar litinin a ƙasar Senegal, mabiya ƙungiyar musulmi ta Baye Fall sun gudanar da bikin tunawa da ranar dawowar wanda ya kafa su marigayi Amadou Bamba daga gudun hijira.
Ma'aikatan gona ƴan Habasha suna girbe gonakin alkama.

Asalin hoton, MOHAMMED HAMOUD / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A Yemen, ma'aikatan gona ƴan Habasha suna girbe gonakin alkama.