Abin da muka sani game da hare-haren na'urar sadarwa kan Hezbollah a Lebanon

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Dubban muatane ne suka jikkata a Lebanon bayan wasu kananan na’urori da ƙungiyar Hezbollah ke amfani da su wajen sadarwa suka farfashe a lokaci guda a faɗin ƙasar ranar Talata.

Aƙalla mutum 12 ne suka rasu sannan 2.800 kuma suka jikkata, inda yawancinsu suka samu munanan raunuka.

Sai kuma a yammacin Laraba, inda aka sake samun fashewar wasu na'urorin sadarwar. Ma'akatar lafiya ta Lebanon ta ce aƙalla ƙarin mutum 14 ne suka mutu sannan wasu 450 suka jikkata.

Ba a dai san yadda aka kai harin ba - wanda ya yi kama da wanda aka tsara. Duk da cewa Hezbollah ta zargi Isra'ila da kai shi, hukumomin Isra'ilar ba su ce uffan ba kan lamarin kawo yanzu.

Ga abin da muka sani zuwa yanzu.

Yaushe kuma a ina lamarin ya faru?

Fashewar ta fara ne a Beirut, babban birnin Lebanon, sai kuma ta karaɗe sauran wurare da dama a faɗin ƙasar da misalin karfe 3:45 agogon ƙasar a ranar Talata.

Shaidu sun ruwaito ganin hayaki na fita daga aljihunan mutane, kafin a ji karamar fashewar da ƙararta ya yi kama da abin tartsatsin wuta da kuma harbin bindiga.

A wani bidiyo da kyamarar CCTV ta ɗauka, an ga yadda fashewar ta auku daga cikin aljihun wani mutum lokacin da ya zo fita daga wani kanti.

An ci gaba da jin ƙarar fashewar har na tsawon sa'a ɗaya bayan wadda ta afku da farko, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

Jim kaɗan bayan nan, mutane da dama suka fara isa asibitoci a faɗin Lebanon, inda shaidu suka ruwaito ganin mutanen cikin kaɗuwa.

Ta yaya na'urorin suka fashe?

Kwararru sun nuna kaɗuwa kan harin na ranar Talata - inda suka ce Hezbollah tana yawan bayyana kanta a matsayin wadda ke ɗaukar matakan tsaro.

Wasu sun ce wata kila kutse da aka yi wa na'urorin ne ya sa suka ɗauki zafi, abin da ya janyo suka farfashe. Ba a dai taɓa ganin abu irin haka ba.

Sai dai kwararru da dama na cewa da wuya irin haka ta faru, inda hotunan fashewar ba su yi daidai da ɗaukar zafi da na'urorin suka yi ba.

Wasu kwararrun sun ce suna ganin an yi amfani da wasu mutane ne wajen kai harin ta hanyar amfani da na'urorin, watakila lokacin da ake harhaɗa su ko kuma wajen kai su ga ita Hezbollah.

Ana cigaba da nuna damuwa kan ƙaruwar amfani da na'urori wajen kai hare-hare a ɓangaren tsaro na intanet a faɗin duniya, inda aka sha ganin irin haka a baya-bayan nan ta yadda masu kutse ke samun damar shiga cikin na'urori tun lokacin da ake ƙera su.

Sai dai waɗannan hare-hare na da alaƙa da manhajojin intanet.

Idan dai har an yi amfani da wasu wajen kai harin to ba gagarumin aiki aka yi ba na yadda aka yi wa na'urorin kutse har ta kai ga fashewarsu.

Security officials in Lebanon say that the pagers were packed with a small amount of explosives months before the devices entered the country. Speaking to the BBC, one ex-British Army munitions expert, who asked not to be named, speculated that the devices could have then been triggered by a remote signal.

Jami'an tsaro a Lebanon sun ce an maƙare na'urorin da wasu abubuwan fashewa watanni kafin a kai su cikin ƙasar.

Wani tsohon jami'in sojan Birtaniya kuma kwararre kan harkar makamai, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya faɗa wa BBC cewa zai iya kasancewa an saka wa na'urorin abin fashewa na sojoji da nauyinsa ya kai kilo 10 zuwa 20, sannan aka ɓoye shi cikin wata na'ura maras inganci.

Abin da muka sani kan waɗanda abin ya shafa?

Wata majiya kusa da Hezbollah ta faɗa wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mutum biyu cikin waɗanda aka kashe ƴaƴan wasu mambobin Hezbollah ne. Sun kuma ce an kashe 'yar wani mamban ƙungiyar.

Cikin mutanen da suka jikkata akwai jakadan Iran a Lebanon, Mojtaba Amani.

Rahotannin kafafen yaɗa labaran Iran sun ce raunukan da ya ji ba su munana ba.

Sai dai shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah bai jikkata ba a fashewar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ta ruwaito. Bayanai sun nuna cewa zai yi jawabi game da harin a yammacin Laraba.

Ministan lafiya na ƙasar, Firass Abiad ya ce yawancin mutanen da suka jikata sun fi samun raunuka ne a hannaye da kuma fuskokinsu.

Da yake tattaunawa da BBC, ya ce: "Yawancin mutane sun samu raunuka ne a fuska musamman ma kusa da idanu da kuma hannaye."

Ya ƙara da cewa: "Mutane da dama da ke karɓar magani suna sanye da tufafin fararen hula ne, don haka da wuya mu iya tantance cewa su ƴan wata ƙungiya kamar Hezbollah ne ko kuma wasu...

"Sai dai muna ganin tsofaffi da kuma matasa cikin mutanen, kamar wani yaro da ya mutu...kuma akwai har da jami'an lafiya.

A wajen Lebanon, mutum 14 ne suka ji rauni a irin wannan fashewa ta karamar na’urar a Syria.

Wa ke da alhaki?

Zuwa yanzu, babu wanda ya ɗauki alhakin kai harin - duk da cewa firaministan Lebanon ya zargi Isra'ila kan hakan.

Firaminista Najib Mikati ya ce fashewar "ta nuna babbar saɓawa da aka yi wa ƴancin ƙasar kuma hari ne mai muni". Wata majiyar tsaro a ƙasar ta zargi jami'an leƙen asirin Isra'ila na Mossad da kai harin, kamar yadda Reuters ya ruwaito.

Wata sanarwa da Hezbollah ta fitar na zargin Isra'ila da kai harin, ta ce tana "ɗora dukkan alhaki na abin da ya faru kan Isra'ila wanda kuma ya shafi fararen hula".

"Isra'ila za ta ɗanɗana kuɗarta kan wannan hari mai muni da ta kai," in ji ta.

Wasu jami'an Amurka da na Isra'ila da ba a bayyana sunayensu ba sun faɗa wa kafar yaɗa labarai ta Axios cewa an tsara ababen fashewar ne. Sai dai a baya-bayan nan, Isra'ila ta fara nuna damuwa kan Hezbollah cewa ta ganoc shirin nata - don haka sai aka kai harin a yanzu.

Jami'an Isra'ila ba su ce uffan ba kan zarge-zargen, sai dai yawancin kwararru sun amince cewa za ta yiwu ita ce ke da alhakin kai harin.

Me ya sa Hezbollah ke amfani da na'urori wajen sadarwa?

Hezbollah ta dogara ne kan amfani da na'urorin a matsayin wata hanya ta sadarwa domin ta yi ƙoƙarin kauce wa gane shirinta daga Isra'ila.

Ana kuma amfani da na'urar wajen aika sakonni, tana kuma ɗauke da wasu lambobi da ake iya yin sadarwa da su.

Tuni aka daina amfani da wayoyin salula saboda fargabar za a iya far wa mutum cikin sauki, ganin cewa Isra'ila ta yi amfani da hanyar wajen kashe Yahya Ayyash da ya kasance ɗan ƙungiyar Hamas da ke haɗa bama-bamai tun 1996, lokacin da wayarsa ta fashe a hannunsa.

Sai dai wani jami'in Hezbollah ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa na'urorin da suka fashe yanzu sabbi ne waɗanda ba a taɓa amfani da su ba a baya. Wani jami'in tsaro a Lebanon ya faɗa wa Reuters cewa sama da na'urori 5,000 aka shiga da su cikin ƙasar watanni biyar da suka wuce.

Mutumin da ya kirkiro kamfanin da ke ƙera kayan laturoni nan na Gold Apollo da ke Taiwan ya musanta cewa kamfaninsa yana da wata alaƙa da dubban kananan na'urorin sadarwa da suka fashe a Lebanon.

Mista Hsu Ching-Kuang, ya ce kamfaninsa ya sanya hannu a yarjejeniya da wani kamfanin da yake Turai da ya ƙera na'urorin kuma ya yi amfani da sunansa.

Lokacin da BBC ta kai ziyara kamfanin a yau Laraba, ta samu ƴansanda na can suna gudanar da bincike a ofisoshinsa.

Shin harin zai iya janyo ɓarkewar rikici tsakanin Hezbollah da Isra'ila?

Hezbollah na ƙawance da abokiyar gabar Isra'ila a Gabas Ta Tsakiya, wato Iran.

Ƙungiyar na takun tsaka da Isra'ila na tsawon watanni, inda suka yi ta aika wa juna makaman roka da makamai masu linzami a baya-bayan nan a faɗin iyakar Isra'ila ta arewaci.

An ɗaiɗata al'ummomi da dama daga ɓangarorin biyu.

Fashewar na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan da majalisar tsaron Isra'ila ta mayar da wasu ƴan ƙasar zuwa yankin arewacin ƙasar da ke fama da yaƙi.

Firaminista Benjamin Netanyahu ya faɗa wa wani jami'in Amurka da ya kai masa ziyara cewa Isra'ila za ta yi abin da ya dace wajen tsaron ƙasarta.

Tun da farko a ranar Litinin, ma'aikatar tsaron cikin gida ta Isra'ila ta ce ta daƙile wani yunkurin kashe wani tsohon jami'inta da Hezbollah ta yi.