Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko Aston Villa za ta dauki fansa a kan Liverpool a Premier?
Aston Villa za ta karbi bakuncin Liverpool a wasan mako na 37 a Premier League ranar Litinin a Villa Park.
A wasan farko da suka kara a Satumbar bara, Liverpool ce ta yi nasarar cin 3-0 a Anfield.
Liverpool, wadda Atalanta ta fitar da ita a Europa League a bana a zagayen daf da na kusa da na karshe tana mataki na ukun teburi da maki 78.
Ita kuwa Villa, wadda Olympiocos ta yi waje da ita a Uefa Conference League zagayen daf da karshe tana ta hudun teburi da maki 67.
Bayanai kan lafiyar ƴan wasa:
Aston Villa na auna koshin lafiyar Youri Tielemans da Nicolo Zaniolo da kuma Alex Moreno, wadanda ba su buga wasanni a baya ba, sakamakon jinya.
An canja Morgan Rogers a wasa da Brighton a makon jiya, sakamakon rauni wanda bai buga gasar Turai ranar Alhamis ba.
Kociyan Liverpool, Jurgen Kloop bai bayyana masu jinya a kungiyar ba a lokacin da ya gana da ƴan jarida.
Sai dai kawai an kwan da sanin cewar Diogo Jota na daf da komawa taka leda.
Wasa tsakanin Aston Villa da Liverpool:
Liverpool ta ci wasa takwas daga tara baya da ta je Villa Park, tun bayan doke ta 7-2 cikin Oktoban 2020.
Wannan shi ne wasa na 100 da Villa za ta karbi bakuncin Liverpool a Villa Park a dukkan karawa, wadda ta yi nasara 40 da canjaras 21 aka doke ta 38.
Aston Villa:
Villa na fatan kammala kakar bana a matakin ƴan hudun farko a Premier League, kuma karo na uku, amma na farko tun bayan 1995/96.
Saura nasara daya ya rage ta yi kan-kan-kan da tarihin da ta kafa a Premier League na cin wasa 21 da nasara 13 a gida a kaka dayam, kamar yadda ta yi a 1992/93.
Wannan shi ne karon farko da kungiyar ta zura kwallo 73 a raga da yawa a kaka, tun bayan 1976-77 da ta ci 76 ta kuma kare a mataki na hudu a gasar.
Liverpool ce kadai da Unai Emery ya fuskanta a matakin koci da bai yi nasara ba a Premier League da canjaras biyu aka doke shi wasa hudu.
Emery bai yi nasara a karawa tara da ya fuskanci Kloop a manyan gasa ba, tun bayan da Sevilla ta ci Liverpool 3-1 a Europa League a 2016.
Ollie Watkins na bukatar cin kwallo daya a lik, ya zama dan wasan Villa da ya ci kwallo 20 a kaka daya tun bayan Peter Withe a 1980-81.
Liverpool:
Wasa biyu Liverpool ta ci a gida daga bakwai a Premier League da ta fuskanci ƴan biyar din teburi har da wanda ta doke Villa.
Karawa daya kacal aka doke Liverpool daga wasa daya a waje na karshe a kakar Premier daga takwas karkashin Jurgen Kloop, shi ne 1-0 a Chelsea a 2018, wadda ta yi nasara biyu da canjaras biyu daga ciki.
Watakila Liverpool ta yi wasa na 10 ana zura mata kwallo a raga a karon farko tun bayan 11 da ta yi a 1998 karkashin Roy Evans.
Mohamed Salah ya ci kwallo bakwai a wasa tara da ya fuskanci Aston Villa a dukkan fafatawa.
Allison zai buga wasa na 200 a Premier League
Ya kamata Kloop ya ci wasa biyu da suka rage ya zama ya yi nasara 300 a matakin kociyan Liverpool a dukkan fafatawa.