Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda jirgin yaƙi ya yi wa ɗan fashi Alhaji Shanono da yaransa 17 ruwan wuta a Kaduna
Rundunar Sojan Sama ta Najeriya ta ce ta kashe wani ƙasurgumi kuma jagoran 'yan fashin daji da ke ayyukansa a Jihar Kaduna mai suna Alhaji Shanono tare da yaransa 17.
An kashe Shanono ranar Talata yayin da yake shirin gudanar da taro da wasu yaransa a garin Ukambo mai nisan kilomita 131 daga birnin Kaduna a arewacin Najeriya, a cewar wata sanarwa daga rundunar.
Daraktan yaɗa labarai na sojan sama, Edward Gabkwet, ya ƙara da cewa dakarun rundunar Operation Whirl Punch ne suka kai harin ta sama bayan tattara bayanan sirri.
A baya-bayan nan, jami'an tsaron Najeriya na kashe jagororin 'yan fashin da dama, ciki har da Albdulkarim Boss da yaransa 27 da aka kashe a ƙarshen makon da ya gabata.
Kazalika, a ranar Juma'a dakarun sojan ƙasa sun ce sun yi nasarar kama ƙasurguman 'yan fashin daji bakwai da masu taimaka musu a jihohin Kaduna da Filato da Nasarawa, duka a arewacin ƙasar.
A gefe guda kuma, 'yan bindigar na ci gaba da kashewa da kuma garkuwa da mazauna ƙauyuka musamman a jihohin arewa maso yamma, inda suke hana manoma zuwa gonaki da kuma saka musu haraji.
Yadda jirgi ya yi wa Alhaji Shanono ruwan wuta
Kakakin sojan sama Edward Gabkwet ya ce Babban Hafsan Sojan Sama na Najeriya Air Marshal Oladayo Amao ya je Kaduna a ranar Laraba don duba ayyukan da rundunare ke yi a yaƙi da 'yan bindiga a arewa maso yamma.
Kuma yayin wannan ziyarar aiki ce kwamandojin rundunoni daban-daban suka bayyana masa nasarar da suke samu.
"Ba zai yiwu mu ajiye makamanmu ba," kamar yadda Oladayo Amao ya shaida wa kwamandojin.
Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce: "Bayan bayanan sirri da muka samu ranar 9 ga watan Agusta cewa Alhaji Shanono ya shirya ganawa da mayaƙnsa a ƙauyen Ukambo, rundunar Operation Whirl Punch ta aika jirgi zuwa wurin.
"Daga sama, an hangi 'yan ta'adda a ƙarƙashin bishiyoyi da ke kan tudu kuma bayan tabbatar da cewa babu gidajen farar hula a wurin, sai aka bai wa dakaru damar kai hari.
"Rahotannin da mazauna yankin suka bayar sun ce an lalata bindiga fiye da 30 da kuma baburan 'yan bindiga 20, yayin da aka kashe 'yan fashi kusan 18, ciki har da Alhaji Shanono, sannan wasu suka raunuka.
"Majiyoyi sun kuma ce an ceto mutum aƙalla 26 da 'yan bindigar suka yi garkuwa da su sakamakon hare-haren."
An kashe 'ƴan ta'adda' suna tsaka da yaƙar junansu
Har wa yau, sanarwar ta ce jiragen soja sun kai ire-iren waɗannan hare-hare a yankin arewa maso gabas, inda suka kashe mayaƙan Boko Haram da na ISWAP suna tsaka da yaƙar juna a Jihar Borno.
"Ɗaya daga cikin irin wannan hare-hare shi ne wanda aka kai ranar 6 ga watan Agusta a Gazuwa mai nisan kilomita 1.2 daga garin Gargash, bayan rahoton sirri da aka samu cewa mayaƙan Boko Haram da ke biyayya ga Shekau da kuma na Islamic State of West Africa (ISWAP) na shirin yaƙar juna.
"Hatsaniyar da suke yi ta ba da damar kai musu harin ba-zata, inda sojoji suka kai hari da jirgi biyu...Kazalika, akwai tutar ISWAP a kan wani gini da aka kafa mai ɗauke da allunan samar da lantarki daga hasken rana."
Rundunar sojan ta ce rahoton sirri ya nuna cewa hare-haren sun yi nasara.