Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An sako ƙarin fasinjojin Abuja-Kaduna bakwai
Maharan jirgin ƙasan Abuja-Kaduna sun sako ƙarin mutum bakwai daga cikin fasinjojin da suka sace a harin da suka kai kan jirgin a watan Maris.
Mai shiga tsakani a sasantawa tsakanin maharan da dangin fasinjojin Malam Tukur Mamu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
Fasinjojin da aka saka din sun hada da mata biyu da namiji daya da kuma yara hudu.
Sanarwar Tukur Mamu ta ce Sheikh Ahmad Gumi ne ya shiga tsakani a wannan karon, tun bayan bayyanar wani bidiyo mako biyu da suka wuce, da ke nuna yadda maharan ke zane fasinjojin.
'Yan bindigar sun sako uku daga cikin fasinjojin kwana biyu bayan bayyanar bidiyon ranar 24 ga watan Yuli.
“Sheikh Ahmad Gumi ya tuntuɓi maharan ta hanyar mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, ya roƙe su cewa su taimaka su saki yaran da iyayensu," in ji sanarwar.
“An fahimci cewa yaran ba su da lafiya kuma yanayin da suke ciki na ƙara taɓarɓarewa tun bayan dukan da aka yi wa mahaifinsu.”
Zuwa yanzu babu tabbaci kan ko an biya kuɗin fansa kafin a sao mutanen, amma rahotanni na cewa na baya da aka saka sun biya miliyoyin naira kafin su samu 'yan cinsu.
Malam Mamu ya yi iƙirarin cewa mahaifin yaran da aka saka ɗin ma'aikacin Hukumar Majalisar Tarayya ne amma babu hannun Majasalisar Tarayyar ko kuma hukumar a sakin nasa.
'Sheikh Gumi da sanata ne suka saka baki'
Tun kafin yanzu Malam Tukur Mamu ya sha bayyana cewa da taimakon shahararen malami Sheikh Ahmad Gumi ake tattaunawa da 'yan bindigar.
A wannan karon ma malamin ya ce da taimakon malamin da wani ɗan Majalisar Dattawa daga arewacin Najeriya aka ceto mutanen.
"Muna sanar da duniya cewa bisa tallafin Sheikh Gumi da kuma wani sanata mai-ci daga Arewa...wanda ya nemia ɓoye sunansa, duka mutum shida sun samu 'yanci a safiyar Laraba.
"Kazalika, an saki wata mace mai shekara 60 mai suna Aisha Hassan, wadda aka ce an sake ta ne saboda dalilai na rashin lafiya mai tsanani."
Sunayen waɗanda aka sako
- Abubakar Idris Garba - mahaifin yaran
- Maryama Abubakar Bobbo - matarsa
- brahim Abubakar Garba - ɗansu mai shekara 10
- Fatima Abubakar Garba - mai shekara bakwai
- Imran Abubakar Garba - mai shekara biyar
- Zainab Abubakar Garba - mai shekara ɗaya da rabi
- Hajiya Aisha Hassan - mai shekara 60