An sauya ranar wasan Arsenal da Brighton a Emirates

An wallafa

Mahukuntan Premier League sun sauya ranar da za a kara tsakanin Arsenal da Brighton a Emirates, domin a nuna fafatawar a talabijin.

Tun farko an tsayar da ranar buga wasan ita ce Asabar 13 ga watan Mayu, yanzu an mayar da shi zuwa Lahadi 14 ga watan Mayu a Emirates.

Kungiyoyin biyu sun fafata a bana a wasan Premier League da kuma League Cup, inda Gunners ta ci 4-2 a Premier, Brighton ta fitar da Gunners a League Cup.

Wasa biyu da suka buga a bana:

Premier League Asabar 31 ga watan Disambar 2022

  • Brighton 2 - 4 Arsenal

EFL CUP Laraba 9 ga watan Nuwambar 2022

  • Arsenal 1 - 3 Brighton

Arsenal tana matakin farko a teburin Premier da maki 72 da tazarar maki takwas tsakaninta da Manchester city ta biyu mai rike da kofin bara.

Brighton wadda ke fatan buga gasar zakarun Turai a badi tana ta shida a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila mai maki 46.

Ranar Asabar 8 ga watan Afirilu, Brighton za ta ziyarci Tottenham a wasan mako na 30, Liverpool kuwa za ta karbi Arsenal ranar Lahadi 9 ga watan Afirilu.

Wasannin mako na 30 da za a buga a Premier:

Ranar Asabar 8 ga watan Afirilu

  • Manchester United da Everton
  • Aston Villa da Nottingham Forest
  • Fulham da West Ham United
  • Tottenham da Brighton & Hove Albion
  • Leicester da Bournemouth
  • Wolverhampton da Chelsea
  • Brentford da Newcastle United
  • Southampton da Manchester City

Ranar Lahadi 9 ga watan Afirilu

  • Leeds United da Crystal Palace
  • Liverpool da Arsenal