Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin ko Super Eagles za ta ci Guinea Bissau kuwa?
Guinea Bissau ta karbi bakuncin Super Eagles a wasa na hudu a rukunin farko domin neman shiga kofin Afirka da za su kara ranar Litinin.
Ranar Juma'a Guinea Bissau ta ci Najeriya 1-0 a filin wasa na Moshood Abiola a wasa na uku a cikin rukuni.
Guinea Bissau ta ci kwallon ta hannun Mama Balde tun a minti na 29 da take leda.
Tawagogin biyu sun kara a gasar kofin Afirka da aka yi a Kamaru a 2022, inda Super Eagles ta ci 2-0, ita ce ta ja ragamar rukuni na hudu a gasar.
Sadiq Umar ne ya fara ci wa Super Eagles kwallon a minti daya da komawa zagaye na biyu, William Troost-Ekong ya kara na biyu, saura minti 25 a tashi wasan.
Bayan da suka buga wasa uku-uku a cikin rukuni Guinea Bissau ce ta daya mai maki bakwai, wadda ta ci Sao Tome da Najeriya da canjaras da Saliyo.
Super Eagles kuwa tana ta biyu mai maki shida, wadda ta yi nasara a kan Saliyo da Sao Tome da rashin nasara a kannun Guinea Bissau.
Ranar Lahadi Saliyo ta je ta doke Sao Tome da ci 2-0 a wasa na uku a cikin rukunin farko.
Jerin 'yan wasan Super Eagles:
Masu tsaron raga: Francis Uzoho (AC Omonia, Cyprus); Victor Sochima (Rivers United); Kingsley Aniagboso (Giant Brillars)
Masu tsaron baya: Oluwasemilogo Ajayi (West Bromwich Albion, England); Bright Osayi-Samuel (Fenerbahce SK, Turkey); Kevin Akpoguma (TSG Hoffenheim, Germany); Kenneth Omeruo (CD Leganes, Spain); Calvin Bassey (FC Ajax, The Netherlands); Daniel Bameyi (YumYum FC); Zaidu Sanusi (FC Porto, Portugal); Bruno Onyemaechi (Boavista FC, Portugal)
Masu buga tsakiya: Wilfred Ndidi (Leicester City, England); Frank Onyeka (Brentford FC, England); Alex Iwobi (Everton FC, England); Joe Aribo (Southampton, England)
Masu cin kwallaye: Kelechi Iheanacho (Leicester City, England); Ahmed Musa (Sivasspor K, Turkey); Samuel Chukwueze (Villarreal CF, Spain); Moses Simon (FC Nantes, France); Ademola Lookman (Atalanta BC, Italy); Terem Moffi (OGC Nice, France); Victor Osimhen (Napoli FC, Italy); Paul Onuachu (Southampton FC, England)
Sauran wasannin da za a buga ranar Litinin:
- Kudancin Sudan da Congo
- Jamhuriyar Afirka da Madagascar
- Niger da Algeria
- Zimbabwe da Morocco
- Angola da Ghana
- Guinea-Bissau da Najeriya
- Habasha da Guinea
- Sudan da Gabon