Ɗan a-waren da ke wasan ɓuya da 'yan sandan Indiya

An wallafa

An takaita amfani da intanet a wasu sassan jihar Punjab da ke arewacin Indiya, tsawon kwana na huɗu a jere yayin da dubban 'yan sanda ke ci gaba da neman jagoran 'yan a-ware ga mabiya addinin Sikh, Amritpal Singh.

Sama da magoya bayansa 100 aka kama a farautar da 'yan sanda suka ƙaddamar tun ran Asabar.

Babban minista, Bhagwant Mann ya yi alƙawarin ɗaukar tsauraran matakai a kan masu yaɗa kalaman ƙiyayya a Punjab.

Mai wa'azin addinin da ake kira Amritpal Singh ya ce yana goyon bayan kafa Khalistan, ko kuma wata ƙasar Sikh ta daban.

Gwagwarmayar Khalistan dai, tamkar wata ƙungiya ce ta 'yan a-ware masu neman ɓallewa da kuma kafa ƙasa ga mabiya addinin Sikh daga jihar Punjab.

Ana tunawa da tasowarsa ne da wani tashin hankali na 1980 a Punjab wanda ya janyo mutuwar dubban mutane.

Har yanzu dai ba a san inda mista Singh ya shiga ba.

A cikin makon jiya ne, wata babbar kotu a Punjab ta buƙaci sanin yadda aka yi mai wa'azin ya tsere wa kamu a lokacin da ƴan sanda ke neman sa.

"Kuma akwai ƴan sanda har 80,000. Ta yaya aka kasa kama shi? wannan gazawa ce,'' in ji kotu, yayin da ta buƙaci gwamnatin jihar ta gabatar da rahoto a kan aikin nemo shi cikin kwanaki huɗu.

Kotun dai tana sauraron ƙarar da lauyan kamfanin mista Singh mai suna Waris Punjab De ya shigar, inda yake zargin an kama mista Singh tare da tsare shi a hannun 'yan sanda ba bisa ƙa'ida ba, inda ya buƙaci a sake shi.

Gwamnati ta ce ta yi ƙoƙarin kama duk waɗanda ake zargi, amma ban da mista Singh.

A ranar Asabar ne, ƴan sandan Punjab suka bayyana shi a matsayin wanda ya gudu bayan ya tsere wa wani kame da aka shirya, inda suka yi ta wasan tsere da mota tsakaninsa da ƴan sanda.

Makusantan mista Singh sun yaɗa labarin yunkurin kama shi kai-tsaye a intanet.

Bayan nan ne kuma, hukumomi suka toshe layukan intanet da takaita aika saƙonni, inda suka tura dubban sojoji zuwa Punjab, yayin da suka fara shirin neman mista Singh a faɗin jihar.

An kama huɗu daga cikin makusantansa da kuma kawunsa, inda aka zarge su da wasu laifuka ƙarƙashin dokar tsaro ta ƙasar - a ranar Litinin ne aka tura huɗu a cikinsu zuwa gidan yarin da ke arewa maso gabashin jihar Assam.

A ranar Talata, gwamnatin Punjab ta ce ta ɗage haramci kan amfani da intanet na ɗan wani lokaci, yayin da ta dakatar da hakan tsawon wani lokaci har zuwa ranar 23 ga watan Maris.

Amritpal Singh ya yi iƙirarin samun ƙwarin gwiwa daga Jarnail Singh Bhindranwale, wani mai wa'azi da gwamnatin Indiya ta zarga da jagorantar ayyukan ta-da-ƙayar-baya don Khalistan.

An kashe Bhindranwale a harin da sojojin Indiya suka kai wani wurin bauta mai tsarki ga ƴan addinin Sikh a1984.

Dirar miƙiya da aka yi wa mista Singh na zuwa ne makonni bayan magoya bayansa sun mamaye ofishin 'yan sanda, suna neman a sako wani mai taimaka masa.

A ranar Litinin, masu goyon bayan kafa Khalistan suka lalata ofishin jakadancin Indiya da ke San Francisco, suna kira a sako mista Amritpal Singh.

An yi irin wannan zanga-zangar a ofishin jakadancin Indiya da ke London ranar Lahadin da ta gabata, inda wani mutum ya cire tutar Indiya daga hawa na biyu na ginin.