Mun kafa cibiyar horarwa kan man fetur - Gwamnan Bauchi Bala Mohammed
Mun kafa cibiyar horarwa kan man fetur - Gwamnan Bauchi Bala Mohammed
An wallafa
Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed ya ce gwamnatinsa ta kafa cibiyar horarwa kan man fetur da aka gano a jiharsa.
Sunan cibiyar Alkaleri Oil and Gas Acquisition Centre, a cewar gwamnan.
Ya ƙara da cewa jihohin arewacin Najeriya sun zuba jarin da ya kai kusan dala miliyan 10 a aikin haƙo man fetur ɗin da aka gano a kan iyakar jihohin Bauchi da Gombe.



