Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal ta ci wasa na biyar a jere a Premier ta bana
Arsenal ta ci gaba da taka rawar gani a gasar Premier ta bana, wadda ta ci wasa na biyar a jere, bayan doke Aston Villa 2-1 a Emirates ranar Laraba.
Wannan sakamakon zai kara jefa kociyan Villa, Steven Gerrard cikin matsi, wanda ya kasa cin wasa hudu daga biyar da ya ja ragama da fara kakar nan.
To sai dai za a iya masa uzuri a wasa da Arsenal, domin ko kusa bai kai shirin da Gunners ta yi ba, kan fara Premier League ta bana.
Gabriel Jesus ne ya ci Arsenal kwallon farko kuma na uku da ya zura a raga a kakar nan, wanda ya koma Gunners daga Manchester City a bana.
Bayan da suka koma zagaye na biyu Villa ta kara sa kaimin da ta farke ta hannun Douglas Luiz.
Minti uku tsakani da aka farke kwallon Arsenal ta kara na biyu ta hannun Gabriel Martinelli, bayan da Bukayo Saka ya buga masa kwallon.
Arsenal ta hada maki 15, ta ci gaba da jan ragamar teburin Premier League, ita ce kadai ta ci wasa biyar a jere da fara kakar nan.