Shugabannin ƙasashen Larabawa za su fara taron neman shawo kan rikicin Gaza

An wallafa

Shugabanni da ministocin harkokin wajen ƙasashen Larabawa da na Turai da dama za su halarci taron zaman lafiya a Masar, inda za su tattauna kan rikicin Gaza.

Daga cikin masu halartar taron harda shugaban Falasɗinawa. Mahmoud Abbas da sarki Abdullah na Jordan da kuam sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres.

Mai masaukin baƙi, Masar ta ce taron zai maayar da hankali ne ga batun tsagaita wuta.

Babu dai tabbatacin cewa taron zai yi wani tasiri ta la’akari da cewa manyan masu ruwa da tsaki a rikicin, Iran da Isra’ila duk ba za su halarta ba.

Wannan na zuwa ne bayan da Hamas ta sako biyu daga cikin mutanen da ta yi garkuwa da su, yayin mummunan harin da ta kai kudancin Isra’ila a farkon watan nan.

Tuni dai Shugaba Biden ya yi maraba da sakin Amurkawan biyu, wata uwa da ɗiyarta

Judith da Natalie Raanan sun zamo mutane na farko da Hamas ta sako, daga cikin waɗanda ta yi garkuwa da su.

Labarin sakin Amurikawan biyu ya fara zuwa ne daga ƙungiyar Hamas, daga baya kuma Amurka da Isra’ila suka tabbatar da shi.

Hamas da kuma shugaba Biden duk sun ce Qatar ta bayar da gagrumar gudunmuwa wajen cimma nasarar sako matan biyu.

Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken ya ce hukumomi na tsara yadda Amurkawan za su samu dukkan kulawar da ta kamata.

Ya ce "Cikin sa’oi masu zuwa za a ba su duk kulawar da ta dace, kuma babu shakka mun ƙosa mu ga cewa mun miƙa su ga iyalan su. Mun yi maraba da sakin su. Mun kuma fahimci halin da ƴan uwa da abokan arzikin su suka shiga."

Mr Biden ya ce ya tattauna da matan biyu ta waya. Ya kuma yi godiya ga Qatar, wadda ta shiga tsakanin don ganin an ceto su.

Mahaifin Natalie Raanan ya shaidawa BBC cewa wannan ce ranar da ta fi kowacce rana muhimmanci a gare shi.

Ya ce yana sa ran komawar ɗiyarsa da matarsa Chicago cikin makon nan.

Rahotanni dai sun ce har yanzu akwai sauran wasu mutum aƙalla ɗari biyu da Hamas ke riƙe da su.