Postecoglou ya yi tir da cin zarafin da aka yi wa ɗan wasansa

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kocin Tottenham Ange Postecoglou ya yi alla-wadai da cin zarafin da ake yiwa ƴan wasan ƙwallon ƙafa a shafukan sada zumunta, ya kuma mara wa ɗan wasan Wales Brennan Johnson inda ya ke cewa zai sami nasarori a ƙungiyar.

An ba da rahoton cewa Johnson ya rufe shafinsa na Instagram saboda sukar da ya sha bayan wasan da Tottenham ta yi da Arsenal a ranar Lahadi, inda ta yi rashin nasara da ci 1-0.

Postecoglou ya ce mai yiwuwa ɗan wasan mai shekaru 23, wanda ya ci wa Spurs ƙwallaye biyar tun lokacin da ya koma daga Nottingham Forest a watan Satumban bara yana fama da rashin ƙwarin gwiwa.

Amma kocin na Tottenham ya ce abin takaici ne yadda cin zarafi a shafukan sada zumunta ya zama ruwan dare gama gari a harkar wasanni.

Spurs ta biya sama da fam miliyan 45 don siyan Johnson bayan da ya yi fice a Forest, inda ya zura ƙwallaye 29 a wasanni 108 da ya buga wa kulob din.

Sai dai ɗan wasan ya yi fama da rashin tagomashi tun lokacin da ya koma arewacin Landan.