Rawar 'yangudun hijira da ciyayya cikin hotunan Afirka

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Wasu daga cikin zaɓaɓɓun hotunan Afirka da na ƴan nahiyar a wasu sassan duniya cikin makon da ya gabata.

Cape Town carnival

Asalin hoton, Chris Jackson / Getty Images

Bayanan hoto, Masu halartar bikin Carnival sun sanya kayayyakin ado a birnin Cape Town ranar Laraba.
Cape Town carnival

Asalin hoton, Chris Jackson / Getty Images

Bayanan hoto, Cape Town na karɓar baƙucin irin waɗannan bukukuwan da dama kowace shekara
Zanga-zanga a Mozambique.

Asalin hoton, Siphiwe Sibeko / Reuters

Bayanan hoto, A ranar Alhamis, wannan mata ta bayyana ɓacin ranta tare da riƙe gwangwanin hayaƙi mai sanya hawaye da jami’an tsaro suka harba kan masu zanga-zanga a Mozambique.
Ƴan sudan

Asalin hoton, Amaury Falt-Brown / AFP

Bayanan hoto, Mutane suna cin abinci bayan sallar Juma'a a wani masallaci da ya sha harbi a birnin Omdurman na ƙasar Sudan.
Sojan Sudan

Asalin hoton, Amaury Falt-Brown / AFP

Bayanan hoto, A babban birnin ƙasar Sudan, Khartoum, wani soja yana neman dakarun ƙungiyar RSF.
Chidimma Adetshina

Asalin hoton, Yamak Perea / Getty Images

Bayanan hoto, Sarauniyar kyau ta Najeriya Chidimma Adetshina tana sanye da rigar furanni a gasar duniya (Miss Universe) da ta gudana a ƙasar Mexico ranar Juma'a.
Mata ƴan gudun hijira

Asalin hoton, Amos Gumulira / AFP

Bayanan hoto, Mata ƴan gudun hijira da ke zaune a tsakiyar Malawi suna rawa a bikin Tumaini ranar Asabar
Mawakiya

Asalin hoton, Amos Gumulira / AFP

Bayanan hoto, Mawaƙiyar Malawi Jetu, mai shekara 72, ita ma ta yi wasa a bikin wanda aka ce shi ne bikin kiɗa ɗaya tilo a duniya da ake yi a sansanin ƴan gudun hijira.
Taron Duniya na Urban Forum a Cairo

Asalin hoton, Mohamed Hossam / EPA

Bayanan hoto, Mata sanye da tufafin da aka sake sarrafa su a taron Duniya na Urban Forum da aka yi a birnin Alkahira.
Tsuntsun da ya shahara a ƙasar Senegal

Asalin hoton, Cem Ozdel / Getty Images

Bayanan hoto, Wannan tsuntsun da ya shahara a ƙasar Senegal ya kasance a wajen gidan wani tsohon mai kama kifi, inda ya kwashe shekara biyar yana rayuwa a birnin Saint Louis
Masu zanga-zanga a Afirka ta Kudu

Asalin hoton, Nic Bothma / Reuters

Bayanan hoto, Masu zanga-zangar adawa da masarautu na adawa da ziyarar Yarima William a Afirka ta Kudu.
Magoya bayan jami'iyyar Change Alliance ta Mauritius

Asalin hoton, Laura Morosol / AFP

Bayanan hoto, Magoya bayan jam'iyyar hamayya ta Mauritius, Change Alliance sun shiga wani gangamin zaɓe a babban birnin ƙasar, Port Louis, ranar Lahadi.