Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matashin koci a tarihin Premier Hurzeler ya fara da cin 3-0
Matashin koci a tarihin Premier League, Fabian Hurzeler ya fara da doke Everton 3-0 ranar Asabar a Goodison Park a karawar makon farko.
Hurzeler mai shekara 31 ya zama matashi a tarihin Premier, bayan da Brighton ta ɗauke shi aiki, bayan da Robert De Zerbi ya ajiye aikin a karshen kakar da ta wuce.
Tun farko, Eveton ta fara zura ƙwallo a raga ta hannun Jack Harrison, amma aka ce an yi satar gida, sannan Joao Pedro ya buga kwallo ta bugi turke.
Brighton ta fara cin ƙwallo ta hannun Kaoru Mitoma, bayan da ya samu tamaula ta hannun Yankuba Minteh, wanda ya fara buga wa ƙungiyar wasa a karon farko.
An bai wa Everton fenariti daga baya rafli, Simon Hooper ya soke, bayan da ya kalli abinda ya faru a talabijin na gefen fili.
Daga baya ne Brighton ta kara na biyu ta hannun Danny Welbeck, bayan da Idrissa Gueye ya yi kuskuren bayar da ƙwallo cikin sauki.
An bai wa Ashley Young jan kati, bayan da ya kayar da Mitoma, inda Simon Adingra ya ci na uku.
Everton ta buga wasan a Goodison Park, inda take fafatawa tun daga 1892, yanzu tana shirin komawa sabon fili a Bramley-Moore Dock a farkon kaka mai zuwa.
Ranar Asabar 24 ga watan Agusta, Brrighton za ta karbi bakuncin Manchester United a wasan mako na biyu.
A dai ranar ta Asabar Everton za ta kai ziyara gidan Tottenhama a karawar ta mako na biyu a babbar gasar tamaula ta Ingila.