Liverpool za ta yi cefane a wannan bazarar - Slot

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kocin Liverpool Arne Slot ya ce har yanzu ƙungiyar na neman ƙarfafa tawagar ƴan wasanta kafin a rufe kasuwar saye da sayar da ƴan wasa.

Reds sun yi ƙoƙarin sayen Martin Zubimendi daga Real Sociedad amma haƙar ba ta cimma ruwa ba bayan ɗan wasan tsakiyar na Sifaniya ya yanke shawarar ci gaba da kasancewa a Sociedad.

Hakan na nufin Liverpool ce kaɗai ƙungiyar Firimiya da ba ta yi wani babban cefane ba a bana, inda za a rufe kasuwar musayar ƴan wasa ranar Juma'a, 30 ga watan Agusta.

Slot ya ce "Na sha faɗi cewa tawagar mu na da ƙarfi sosai kuma ba abu ne mai sauƙi ba a sami ƴan wasan da za su taimaka mana wurin ƙarfafa ƙungiyar."

"Maganar gaskiya ita ce, Zubimendi yana ɗaya daga cikinsu, amma ya yanke shawarar cewa ba zai zo ba, za mu ci gaba da ƴan wasan da muke da su. [Wataru] Endo ya yi ƙoƙari sosai a wasannin share fage don haka muna cikin yanayi mai kyau.

"A bayan fage, [Daraktan wasanni] Richard [Hughes] na ƙoƙarin ƙarfafa tawagar , amma dai abin takaici shi ne Zubimendi ya yanke shawarar zama a inda ya ke.

"Ya yi duk ƙoƙarin kawo shi amma, idan ɗan wasa ya yanke shawarar ba zai zo ba, to a fili yake ba zai zo ba."

Slot ya maye gurbin Jurgen Klopp a matsayin kocin Liverpool bayan Bajamushen, wanda ya jagoranci Reds zuwa gasar cin kofin Carabao da kuma matsayi na uku a gasar bara, ya bar kulob ɗin a ƙarshen kakar da ta gabata.

Wasan Liverpool na farko da zai jagoranta zai kasance ne a Ipswich Town ranar Asabar, 17 ga watan Augusta.