Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rundunar 'yan sanda ta yi kira a dakatar da zaben kananan hukumomi na jihar Osun
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bukaci gwamnatin jihar Osun ta dakatar da shirin gudanar da zaben.
A yau ne dai ya kamata a gudanar da zaben kananan hukumomi na jihar Osun.
A cikin wata sanarwa da rundunar 'yan sandan Najeriya ta fitar ta ce ta samu bayanan sirri masu sahihanci da ke nuni da cewa za a iya samun tashin hankali idan aka gudanar da zaben kananan hukumomin a jihar ta Osun.
Sanarwar da ta wallafa a shafinta na X da ke dauke da sa hannun kakakinta ACP Olumuyiwa Adejobi ta ce bisa la'akari da barazanar da ake fuskanta na tsaro rundunar 'yan sandan ta shawarci gwamnatin jihar Osun da ta dakatar da gudanar da zaben nan da nan domin kare lafiyar al'umma da zaman lafiyar kasa.
"Rundunar 'yan sandan Najeriya ta samu sahihan bayanan sirri da ke nuna akwai yiwuwar tashe-tashen hankula da kuma babbar barazana ta tsaro idan zaben kananan hukumomin da aka shirya gudanarwa a jihar Osun'' .
''Bayan nazari kan yanayin tsaro da ake ciki a yanzu tare da tabbatar da cewa idan aka gudanar da zabubbukan a cikin wannan yanayi mara kyau to zai iya rikidewa zuwa tashe-tashen hankula, tare da yin barazana ga rayuka da dukiyoyi''.
Ta ce ya zama wajibi a yi la'akari da bayanin da lauyan gwamnatin tarayya da ministan shari'a na kasar ya bayar a kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a kan tsarin tafiyar da kananan hukumomi a jihar Osun a ranar 10 ga watan Fabrairun 2025 wanda ya tsaya tsayin daka wajen soke hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke a baya, wanda kuma ya kara tabbatar da cewa zaben zai kasance mara inganci saboda ya sabawa doka .
To sai dai a dayan bangaren gwamnatin jihar Osun ta yi watsi da shawarar.
A sanarwar da kwaminisan yada labarai na jihar Oluomo Kolapo Alimi ya fitar ya ce :''Gwamnatin jihar Osun ta ji kiran na rundunar 'yan sandan Najeriya amma tayi nadamar sanar da cewa ta yi watsi da shawarar saboda ta na bin doka da oda''.
''Gwamnatin jihar a karkashin Gwamna Ademola Adeleke ya yi nazari kan shawarwarin inda ta kai ga yanke shawarar cewa shawarar hedkwatar rundunar ta nuna son kai, bangaranci da kuma saba wa tsarin dimokuradiyya''.
Tun farko gwamnan jihar , Osun Ademola Adeleke ya lashi takobin cewa ''ba bu gudu ba ja da baya '' zai gudanar da gudanar da zaben kananan hukumomin da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar tsara yi a ranar 21 ga watan Fabarairu.
A baya baya nan ne Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta nemi gwamnatin ƙasar ta ƙakaba dokar ta-ɓaci a jihar Osun sakamakon rikicin siyasar da ya janyo mutuwar mutum shida.
Jam'iyyar PDP mai mulki a jihar ta Osun ta ce kiran a saka dokar ta-ɓaci wani abu ne da ke nuna gazawa daga ɓangaren jam'iyyar ta APC.
Jam'iyyun biyu dai na ta sa-in-sa tare da ɗora laifi ga junansu dangane da rikicin da ya haifar da rasa rayukan mutum shida.